Imamanci Da Nassi



Dabari ya rawaito cewa Usman ya aikawa Mu’awiya da Abdullahi dan Sa’ad dan Abi Sarh, da Sa’id dan Asi, da Amru dan Asi, da Abdullahi dan Amir, sai ya tara su domin ya yi shawara kan al’amrinsa, sai ya ce da su: Kowane mutum yana da wazirai da masu ba shi nasiha, kuma ku ne waziraina masu ba ni nasiha kuma aminaina, kuma kuna ganin abin da mutane suka gani na in kawar da gwamnonina, in kuma mayar da dukkan abin da da suke ki zuwa ga abin da suke so, ku yi kokarin dubawa ku ba ni shawara.

Yayin da suka ba shi shawara sai ya yi aiki da duk shawararsu; ya kuma mayar da su a kan ayyukansu, ya kuma umarce su da tsanantawa ta fuskacinsu, da kuma korar mutane kan iyakoki[33] da kuma hana su komawa wajan iyalansu, ya kuma yi niyyar hana su albashinsu domin su bi shi su bukace shi[34]. Wannan irin al’amura masu karo da juna mustahili ne a same su a nazari daya, ta yadda zai zama nazari mai dacewa da al’amuran tafiyar da sha’anin al’umma da yake da doka da ake iya fahimta. Kuma daidai gwargwadon kokawanto game da ingancin wannan nazari daidai yadda yake kai wa ga rinjayar da dogaro da ingancin nassin shari’a da ya zo daga Annabi (S.A.W) wajan ayyana halifansa.

Wannan ita ce irin natijar da Dr. Ahmad Mahmudu Subhi ya cimma yana mai duba nazarin imamanci yayin da ya ce: “Amma ta nahiyar tunani Ahlussunna ba su kawo wani nazari mai karfi ba game da siyasa da zai iyakance ma’anar bai’a da shura da ma’abota nada shugabanci da warwarewa daga manyan al’umma, balle a samu wani abu mai iya bambance mana tsakanin mahanga da abin da ya faru a aikace a zahiri, ko tsakanin abin da yake na shari’a da kuma abin da ya gudana a tarihi a aikace.

Sai ga nazarin Ahlussunna a siyasa ya bayyana a wannan zamanin karshe bayan daula ta tsayu a kan wanda ya fi karfi ya yi mulki kamar yadda ya zo a mafi yawancin wannan ra’ayoyi sun zo ne domin raddi ga nazarin Shi’a mabiya Ahlul Baiti (A.S), Kuma wasu daga wadannan ra’ayoyi aka sanya su a matsayin dalilai na hukuncin shari’a saboda dogaro da usulubin da halifofi uku na farko suka yi shugabanci.

Wannan kuma ci baya da faduwa da rashin makama tsakanin shari’a da kuma abin da ya faru game da halifanci ne, balle kuma ga maganganu masu karo da juna na wadannan ra’ayoyi da abin takaici daga karshe suka sanya su a cikin dokokin fitar da hukuncin shari’a. Ba komai ne hadafinsu na yin haka ba sai samar da wani ra’ayi mai kishiyantar mahangar Ahlul Bait (A.S) na samun tabbatar nassi a game da halifanci[35].

Na uku: Muhimmancin da shari’a ta bayar ga abin da shawara ta zartar da kuma alakarsa da halifancin da yake da nassi. Zamu ga mafi muhimmanci madogarar shari’a da wannan nazari na shura ya dogara da shi ita ce wannan aya mai girma ta: “Ka yi shawara da su kan al’amari”.

Wannan aya tana lizimta wa shugaba wajabcin shawara a kan wani ra’aryi gun wadanda suke ganin ana magana da Manzo ne da umartarsa da yin shawara, kuma umarni yana nuna wajabci, wannan kuwa yana nuna wajabcin shawara da musulmi, kuma tunda ba za a iya shawartar dukkan musulmi ba gaba daya to wannan yana nuna shawara da ma’abota ra’ayi da tunani na wannan al’umma ne[36].

Da wannan ma’anar zamu iya tambaya cewa; Shin shawara tana nufin ana neman yin ta a kan kanta, ko kuma ita hanya ce da za a cimma wasu hadafofi da ita?

 Suka ce: Ba makawa shawara ba a nemanta a kan kanta kuma ba tana zaman kanta ba ne, ita shawara hanya ce ta tabbatar da wasu abubuwan da mafi muhimmancinsu sanin ra’ayin wasu da kuma tunaninsu da tattaunawa, Domin idan tunani ya zo daga mahanga daban-daban aka tara shi waje daya sai ya sami kima mai girma wajan sanin makamar siyasa, da hukunci, da kuma tafiyar da al’amura, da tattalin arziki, da aminci, da yaki, a wannan kasa, wannan kuwa yana tabbata ba tare da ma’asumi ba daga ma’abota shugabanci.

A nan hadafin sanya shawara zai bayyana, sai dai menene matsayin shura a shari’a? Kuma shin natijar da za a samu ta hanyar shawara da ijma’i ra’ayin duka ake bukata ko kuma ra’ayin mafi yawa za a dauka? Kuma shin ya zama dole ga shugaba ya yi riko da wannan ko kuwa?. Malaman Ahlussunna suna bayar da amsa kala biyu ne a kan hakan:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next