Imamanci Da Nassi



Kawai wannan domin gyara abin da ya faru ne a tarihi da kuma neman ba shi halacci na shari’a da kuma neman kare kurakuran magabata na farko daga tuhumarsu daga wannan aiki mai hadari da suka gabatar ba tare da wani dalili na shari’a ba, da kuma neman wanke su daga munanan sakamakon abin da wadannan ayyuka na su suka haifar a sakamakon haka. Saboda haka ne ma kallafawa kai bayani da nema musu uzuri ya bayyana a wannan nazari kamar yadda yake a fili, wannan kuma saboda:

1- Kowanne daga wadannan hanyoyi uku babu wani dalili na shari’a da ya dogara da shi gaba daya, hatta da malamai daga sahabbai ba su san shi ba a bisa hakika.

2- Asalin shura da aka fada a fuska ta farko wanda aka samu daga bai’ar da aka yi wa Abubakar bai faru ba a bai’arsa, kuma ba wanda ya taba da’awar hakan, har ma Umar ya ambace ta da cewa ita bai’ar kuskure ce ba tare da shawara ba, Sai dai wadanda suka zo daga baya sun ba da surar shura domin su ba ta sabon tufafi na shari’a a zabar halifa na farko, wasu ma sun so su ba ta siffa na ijma’i[14].

3- Tsoron faruwar fitina ya zama uzuri da aka zaba wajan wanke farkon bai’ar da aka yi ga halifa na farko yayin da wannan ya faru ba tare da shawara ba, ba a kuma saurari manyan sahabbai ba daga Muhajirun da Ansar wadanda ya kamata su tsinkayi wannan uzurin da aka bayar na gaggautawa domin tsoron sabani da fitina ba, wannan kuwa ya bayyana a nassin hadubar Umar.

Sai dai abin mamaki! Sai ga fitina din ta zo ta dawo hanyar shari’a da ake amfani da ita wajan zaban halifa kamar yadda muka yi bayani a hanya ta uku, ta yadda ake ganin hatta da sa karfi da mamaya da rinjaye da takobi hanyoyi ne na kai wa ga halifanci, kuma wanda ya yi galaba shi ne halifa na shari’a kuma wajibi ne a bi, kuma wannan hanya budaddiya ce ga duk wanda yake mai kwadayi. Ashe akwai wata fitina da ta wuce wannan?!

Na Biyu: Nassin Halifanci Ya Zo Daga Manzo

Farra’u a littafin Ahkamus suldaniyya yana cewa: Babu jayayya a kan tabbacin hakkin halifa a kan wasiyya ga wanda zai maye gurbinsa, kuma babu kokwanto a kan zartuwar wannan wasiyya, domin imami shi ne ya fi cacanta ta da ita, zabinsa yana ga abin da ya zartar kuwa wannan ba ya dogara da ma’abota ra’ayi da fada aji na al’umma[15], wannan yana zama na halifa ne saboda tsoron faruwar fitina da kuma rashin zaman lafiyar al’umma[16] saboda haka wasu daga sahabbai suka rika koma wa Umar dan Khaddabi suna tambayarsa ya yi wasiyya ga wanda zai maye gurbinsa[17].

Ibn Hazam ya karfafi wannan ya ce: Mun samu cewa nada jagoranci yana inganta ta wasu fuskoki:

Na farko kuma mafi inganci mafifici shi ne shugaba mai mutuwa ya yi wasiyya zuwa ga wani mutum da yake zaba shugaba bayan mutuwarsa, shin ya yi hakan a lokacin lafiyarsa ko lokacin mutuwarsa ne, kamar yadda Manzo ya yi ga Abubakar, ko kuma Abubakar ya yi ga Umar, ko kuma Sulaiman dan Abdulmalik ga Umar dan Abdul’Aziz.

Ya ce: Wannan fuska da muka zaba waninmu ya yi musunta, kuma mun zabe ta ne saboda abin da yake cikinta ne na cigaban saduwar jagoranci ba katsewa, da kuma tsaruwar al’amarin musulunci da ahlinsa, da kuma dauke abin da ake tsoro na sabani da rikici da ake zaton faruwarsa na daga rashin zaman lafiya, da kuma tsoron kada sirri ya yadu kuma kwadayin wasu ya tashi[18], Sai dai nassi da aka yi da’awrsa ga Abubakar daga Manzo bai tabbata ba, domin babu nassi ga Abubakar shi a kan kansa da cewa shi ne shugaba bayan Manzo (S.A.W), kai ba ma wanda ya taba cewa akwai shi, kai al’umma sun hadu a kan ma babu shi, domin duk wanda yake son ya tabbatar da nassi ga Abubakar to dole ya kore al’amarin da ya faru a Sakifa a dunkule da kuma a rarrabe, kuma ya karyata duk abin da ya zo a sihah na maganar Abubakar, da Umar, da Ali, da dan Abbas, da Zubair, game da halifanci. Saboda haka dole ya rusa dukkan abin da a zo na daga nazarin Ahlussunna game da Manzo (S.A.W) da imamanci, wannan nazari ba a gina shi a kan asasi daya, wato bai’a ga Abubakar ta wannan hanya da ta faru a Sakifa da kuma abin da ya biyo baya! Amma daga faruwar wannan abu ne nazarin shura ya samo asali tsakanin manyan al’umma, saboda haka babu wani ijma’i da ya tabbata, ijma’i a kan nassi game da Abubakar korarre ne[19]”.

A nan ne Gazali ya kawo wata magana mai daidai da wannan ijma’i yana mai rushe maganar Ibn Hazam, Gazali yana fadi da alamar tambaya cewa: Don me ya sa ba ku ce nassi wajibi ne ya zo daga Annabi ko kuma daga halifa ba domin ku yanke cibiyar sabanin da ake yi?



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next