Mace a Inuwar Musulunci



Muna iya fahimtar cewa girman wannan aya ba kawai daga abin da ta kunsa na manyan ma'anoni ba ne, a'a har

ma daga bude Surar Nisa'i, wadda ke magana game da sha'anonin mata, da wannan aya; wadda kuma take cikin manyan surori, da d'aukar wannan aya a mastayin asasi da mabubbugar tunani da shar'ancin Musulunci wadanda suka tsara alaka tsakanin namiji da mace, suka kuma iyakance matsayinta da gudummawarta a cikin al'umma.

2-Asasi na biyu da ya wajaba a yi nazarin shi a bisa asasin alaka tsakanin namiji da mace shi ne alakar so, kauna, tausayi, tabbaci da natsuwar zuci, wad'anda suka misaltu a fadar Allah Madaukaki:­

"Akwai daga ayoyinSa Ya halittar muku mata daga kanku, don ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya kauna da tausayi a tsakaninku, lalle cikin wannan akwai ayoyi ga mutanen da ke tunani." Surar Rumu 30:21. 3- Daidaitawa cikin hakkoki da wajibai:­

"..kuma suna da hakkoki a kan mazajensu kamar (yadda mazajensu ke da hakkoki) a kansu da kyautatawa.." Surar Bakara, 2:228.

Wannan yana nufin cewa kowane daya daga namiji da mace akwai hakki na wajibi da ya hau kanshi kuma ya zama wajibi ya aiwatar da abin da ya hau kanshi game da dayan da kyautatawa da zamantakewa mai kyau. Da wannan Musulunci ya auna kuma ya tsara a sasan alaka da wannan ka'ida ta shari'a da halayya makadaiciya, sai ya tabbatar da mafi daukakar ka'ida ga hakkin mace.

4-Amma alakar zamantakewa tsakanin namiji da mace, ita ce alakar kauna kamar yadda AIKur'ni mai girma ya fada: "Muminai maza da muminai mata kuwa, masoya

juna ne.."

Alkur'ani na bayar da wannan kyakkyawar sura ta alakar namiji da mace a al'umma da cewa ita ce alakar kauna, wadda ta hada mafi girman so da girmamawa, kalmar (ط§ظ„ظˆظ„ظ‰) da ayar ta yi amfani da ita da larabci, tana nufin: mai taimako, masoyi da aboki,da wannan za mu fahimci kimar managarciyar mace, da ita da namiji daidai ne a wannan bayani na Alkur'ani.

Wani abu na zamantakewa da za a iya ganin shi a duniyarmu ta yau wadda ta kaskantar da kai ga mulkin mallaka, danniya da fin karfin dagutai, shi ne bayyanar danniya, fin karfi da mamaya, tasirin wadannan ya bayyana a cikin mu'amalar zamantakewa da tarbiyya a makarantu da gidaje da alakokin ayyuka da tsare-tsaren zamantakewa ta surori dabam-dabam.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next