Mace a Inuwar Musulunci



"Ya Ubangiji, Ka gafarta min ni da mahaifana da kuma wadanda suka shigo gidana suna masu imani, da kuma (sauran) Muminai maza da mata, kuma ka da Ka kari kafirai da komai face

halaka". Surar Nuhu, 71:28. "Ranar da za ka ga Muminai maza da muminai mata haskensu na tafiya a tsakaninsu.."

Surar Hadidi, 5'l:l?.

A wadannan ayoyi AIKur'ani ya daga mace zuwa mafi girman matsayi da mutun zai iya kai wa a duniya da lahira, shi yana mu'amala da ita da dan'uwanta namiji daidai wa daida; ita da namiji a fahimtar sakon Musulunci masoya juna ne da soyayya ta akida, suna aikin gyara al'umma, da yaki da barna, laifuka da lalacewa, suna daukar sakon alheri da zaman lafiya da gina fcasa.

A aya ta biyu Annabi Nuhu (a.s.) ya fuskanci Ubangijinsa da addu'a ga Muminai mata kamar yadda ya fuskance Shi da addu'a ga Muminai maza; daga abin da wannan ganawa (da Ubangiji) ta kunsa; asasan karimci, kauna da girmama mace na fitowa, wannan kuwa saboda yin addu'a ga wani dauke da dukkan wadannan ma'anoni.

Matsayin mace na kara haske da tartsatsi mai tsarki a shafukan Alkur'ani ta hanyar surantawarsa ga Muminai maza da Muminai mata a wani sarari na haske, ranar haduwa da Ubangiji, sa'ar cancantar sakamakon da ayyana makomar mutum ta hanyar ayyukansa da tafiyarsa a rayuwa.

Haka muke fahimtar cewa AlKur'ani ya ba managarciyar mace kauna da soyayya, ya kuma yi mata addu'a da gafara, afuwa da rahama; ya kuma kewaye ta da sarari na haske; misalinta ita ce Asiya matar Fir'auna, Maryamu mahaifiyar AlMasihu, Khadija matar Manzon Allah (s.a.w.a.) da Fadimatu 'yar Muhammadu (s.a.w.a.).

Za mu riski girman mace a sakon Musulunci da rayuwar Manzon Allah (s.a.w.a.) ta hanyar da ta daukaka mutuntakarta, ya yabe ta da girmamawa; idan muka san cewa farkon wanda ya yi shahada a Musulunci ita ce Sumayya, mahaifiyar babban Sahabin nan Ammar bin Yasir, jagoran shirka Abu Sufyan ne ya kashe ta. Hakika ta bayar da rayuwarta ga asasan sakon Musulunci, a lokacin da fito-na-fito ya fara tsakanin 'yan ta'adda da dagutai (a wani bangare), da Muahammadu (s.a.w.a.) da wadanda aka raunana da bayi, wadanda suka sami sakon Musulunci mai kwato hakkin dan Adam, mai 'yanto mutane daga jahilci da danniyar mutum ga dan'uwansa mutum (a daya bangaren).

Haka nan da yawa daga matan da aka raunana sun yi gaggawa wajen gaskata Annabi (s.a.w.a.) a farkon kiransa, sun jure cutarwa, azabtarwa da wahalhalu. sun yi hijira zuwa Habasha da zuwa Madina, sun taimaki Allah da ManzonSa (s.a.w.a.) da duk karfin da suke da shi.

Mutuntakar managarciyar mace za ta kara kyautata lokacin da muka shiga sararin nan da ke cike da Shahidai ta hanyar surantawar AIkur'ani da labarinsa da ya bayar da cewa:­



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next