Mace a Inuwar Musulunci



"Kuma kasa ta haskaka da hasken Ubangijinta, aka kuma ajiye takardu (na ayyuka), kuma aka zo da Annabawa da Shahidai, aka yi hukunci a tsakaninsu da gaskiya, alhali su ba za a zalunce su ba".

Surar Zumari, 39:69.

Lalle mace Musulma ba ta gano matsayinta na hakika a Musulunci ba tukuna, haka nan namiji Musulmi bai san matsayin mace a Musulunci a bisa hakikanin shi ba tukuna;

don haka ma'aunin mu'amala da alaka suka gurbace, irin wanda ba ya tabbata sai an dawo zuwa ka'idojin Alkur'ani don kowane daga cikinsu ya san hakkinsa da matsayinsa da nauyin da ya hau kansa a kan dayan, da alakarsa da shi.

Macen da ke haniniya a bayan hohon nan na wayewar abin duniya na zahiri wanda babu abin da ke bayansa face mafada da wulakanci ga mace.da ta san abin da ke cikin Musulunci na kima da hakki, da ba ta kira komai ba in ba Musulunci ba. kuma da ta san cewa abin da zai ceto karamarta da hakkinta su ne ka'idojin Alkur'ani.

TANADIN MACE DON CIKA AIKINTA

Shiri da tarbiyya na da tasiri mai karfi wajen gini da hada mutum da aikinsa a cikin al'umma, da fuskantar da iyawarsa da kokarinsa zuwa mafuskanta ta gini mai kyau. A halin yin watsi da mutum da hana shi tarbiyya da fuskantarwa, da tanaji mai tsari kuwa, zai sa ya tashi sakakke, wanda yanayi da fare-fare ke galaba a kan shi, irin wad'anda a galibi suke musabbabin lalacewar mutum da tafiyar kokari da kwarewarsa da yi wa ci gaban zamantakewa tangarda; daga nan sai mutum ya zama mai rauni sukurkutacce, baya iya mu'amala da al'umma da fare-fare da matsaloli da damammaki da mu'amala mai nasara.

Surar nan ta misali a Musulunci wadda ya wajaba ta yi nazarin yanayin mace ta hanyar ta, ita ce surar mace a cikin AIKur'ani da sunna, wadda kuma ke tsaye a kan asasai masu yawa kamar haka:­

1-Kadaitar Nau'in dan Adam: Wadda ta ginu a kan asasin fadar Allah Madaukaki:­

"Ya ku mutane, ku ji tsoron Ubangijinku, wanda Ya halicce ku daga rai guda daya (Adamu), Ya kuma halittar masa mata (Hauwa'u) daga gare shi, Ya kuma baza maza da mata masu yawa daga gare su. Ku ji tsoron Allah Wanda kuke tambayar (taimakon junanku) da Shi, kuma (ku ji tsoron hakkokin) zumunta. Hakika Allah Ya kasance Mai kiwo ne a gare ku". Surar Nisa'i, 4:1.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next