Mace a Inuwar Musulunci



MACE A INUWAR MUSULUNCI

Ina Dalilin Sukar Matsayin Musulunci Game Da AI'amarin Mace?

Nazarin wannan al'amari (na hakkokin mace a Musulunci) na daga cikin manyan al'amurra na tunani da wayewa a wannan lokaci da muke ciki. Masu fada da Musulunci, `yan amshin Shatansu da wad'anda suka jahilci tunane-tunanen Musulunci, basu gushe ba suna ci gaba da kai hare-harensu na zalunci a kan tunane-tunane da shar'ance-shar'ancen Musulunci, suna masu ikirarin cewa an zalunci mace a Musulunci.

Ta hanyar nazari da bin diddigin asasan wannan yaki na tunani (game da hakkokin mace) tsakanin Musulunci da akidar abin duniya na zahiri da bai yi imani da addini ba, zai bayyana mana cewa tsaikon ka-ce-na-ce din duk ya kewayu ne a kan wani al'amari na asasi, shi ne tunanin rashin imani da addini da ke kirazuwa ga sakewa da kwance duk wani kaidi ga jima'i; wato wannan ra'ayi da a cikin shi mace ta zama wata na'urar jin dadi da biyan bukatun jaraba, wad'anda ke haifar da wargajewar iyali da al'umma da mace. Alhali kuwa Musulunci na kira zuwa ga karrama mace da dage wannan matsayi na wulakanci, da ba ta hakkoki da matsayin da suka ba ta daman yin kafada da kafada da namiji wajen gina rayuwa, da bayyana mutuntakarta a kan asasin 'yan Adamtaka madaukakiya, wadanda za mu yi bayaninsu a takaice a wannan babin.

Kafin mu fara magana a kanwannan babi, ya kamata mu bayyana manyan sabubban wannan ka-ce-na-ce (na hakkokin mace), da dalilan sukan Musulunci na cewa ya tauye mata hakkokinsu.

Marubuta, manazarta, masu da'awa zuwa ga Musulunci, malamai da kungiyoyin kira da wayarwa ta Musulunci, masamman ma wadanda ke zaune a kasashen da ba na Musulmi ba, masamman a kasahen Turai da Amirka; dukkansu suna aiwatar da wajibin da ya hau kansu na bayanin wannan mas'ala mai muhimmanci ta hanyar bincike-bincike, nazarce-nazarce, da tarurrukan karawa juna ilimi a dukkan fagage, na siyasa, halayyar dan Adam, zamantakewa, iyali da zaman gari dabam-dabam.

Mafi girman dalilan da ke boye a karkashin wad'annan hare-hare da ake yi wa tunane-tunanen Musulunci a wannan fage, ana takaitasu cikin abubuwa masu zuwa:­

1-Ta'allaka wasu al'adu da suka ci baya da nazarin zamantakewa a Musulunci: Daga cikin al'amurra na asasi da ya wajaba a kan marubuta, wayayyun Musulmi da masu kira zuwa ga Musulunci su yi bayaninsu, akwai kuskuren da masu jayayya da Musulunci ko wadanda suka yaudaru da tunanin abin duniya na zahiri ko wadanda ma'anoni suka cakude musu kuma mummunar fahimta ta yi galaba suke yi, wannan kuwa shi ne cakudawa da rashin rarrabewa tsakanin abin da Musulunci ya ginu a kai na halaye da ka'idoji na Musulunci, da al'adun zamantakewa na ci baya da suka taso a wasu kasashen Musulmi da ba su waye ba. wadanda kuma suke sabawa ruhin Musulunci da ka'idojinshi da tsare-tsaren zamantakewa da alakokin jima'i da asasan alaka tsakanin namiji da mace; don haka sai suka shiga danganawa Musulunci -bisa jahilci ko da gangan- duk abin da suke shaidawa a kasashen Musulmi. A nan babu makawa mu yi ishara ga bambancin da ke tsakanin yadda al'ummar Musulmi take a halin yanzu da yadda ya kamata al'ummar Musulmi da ke tsaye a kan asasan Musulunci take, mun kuwa riga mun yi ta'arifin (bayanin ma'anar) al'ummar Musulunci.

Hakika wannan ci baya na zamantakewa da al'ummar Musulmi ke fama da shi, wani yanki ne na gamammen ci baya a fagagen ilimi, sannai, bunkasa, masana'antu, lafiya da saurarnsu.

Mummunan surar da wasu masu bincike game da zamantakewa ke cirowa daga yanayoyin zamantakewa dabam-dabam, kamar nazarin nan da aka gudanar a kan yanayin zamantakewar mace a kauyen Masar ko Iraki ko Maroko ko yankin saharar tsibirin larabawa da wasunsu; duk suna fitar da matsalolin mace ta hanyar hangen kauyanci da sahara wadanda suka ci baya kuma suke zaluntar mace.sa'an nan sai wadannan nazarce-nazarce suka shiga bayar da misali ga zamantakewar Musulunci da su.saboda mutanen wadannan wurare Musulmi ne. sun gafala da cewa wadannan tunane-tunane da ayyuka ba su da wata alaka da tunane-tunanen Musulunci da ayyukansa. kuma ba kawai suna karo da halayya da hukunce-hukuncen Musulunci ba ne. a'a har ma Musulunci ya kebe wani sashe daga tunane-tunanensa da dokokinsa da halayyarsa don yaki da su da sauya su.

2-Jahiltar Musulunci: Daga cikin matsalolin da ke tunane-tunanen Musulunci ke fuskanta a wannan lokaci da muke ciki, akwai jahiltar Musulunci da wasu ke yi, masamman ma a kasashen Turai, Amirka da sauran nahiyoyin da ba na Musulunci ba. Wadannan na jahiltar mafi karanci daga ka'idojin Musulunci.kai! suna ma yi mishi wata mummunar fahimta karkatacciya da ke siffanta Musulunci da siffofin: bata, ta'addanci, zubar da jini, ci baya da tsattsuran ra'ayi. Wadannan tunane-tunane na daga abubuwan da kungiyoyin Mustashrikai (masanan Turawa da su ke karantar halayyar kasashen Musulmi da addinin Musulunci don manufofi dabam-dabam), Sahyoniyawa(kungiyar Yahudawa masu tsaurin ra'ayi).da kungiyoyin Coci-Coci da mishan-mishan na Majami'an Kiristoci suka sana'anta.



1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next