Karfafa Ginin Al'umma



Kudura,Aniya da Kafewa

Na Biyu: Shura tana a matsayin kudura da kafewa wajen aiki, saboda – a dabi’ance – mai neman shawarar zai sami kwanciyar hankali da kafewa kan matsayar da ya dauka da kuma aikin da yake son aikatawa bayan shawarar.

An ruwaito daga Imam Sadik (a.s) daga mahaifinsa Muhammad bn Ali al-Bakir (a.s) yana cewa: “An ce wa Manzon Allah (s.a.w.a): mene ne kudura? Sai ya ce: neman shawarar ma’abuta ra’ayi da kuma binsu[34]”.

MafiKyaun Tafarkin Sanin Hakika

Na Uku: Shawara tana daga cikin mafi kyawun tafarki da hanyar isa ga hakika, saboda mutum zai isa ga hakikanin lamari ta hanyar ra’ayin masana nesa ba kusa ba daga soyace-soyacen zuciya, wanda me yiyuwa ne su sami matsuguni cikin zuciyar mutum da za su sanya shi dogara ga wani ra’ayi ko matsaya ko kuma wani aiki na musamman.

Akwai hadisan Ahlulbaiti (a.s) da suke magana kan wannan batu, kamar yadda aka ruwaito Amirul Muminina (a.s) cikin Nahjul Balaga yana cewa: “Wanda ya yi aiki da ra’ayinsa kawai ya halaka, wanda ya nemi shawarar mutane ya kasance tare da su cikin hankulansu (fahimtarsu)[35]”.

A bayan mun kawo maganarsa ta cewa: “Neman shawara ita ce asalin shiriya”.

1-     Al-Barki ya ruwaito Imam Sadik (a.s) yana cewa: “Ka nemi shawarar mai hankali daga cikin ma’abuta tsantsaini, saboda ba ya umarni da wani abu face alheri, ina gargadinka da kada ka saba masa saboda saba wa mai hankali mai tsantsaini ya kan haifar da gibi a addini da kuma duniya[36]”.

Amirul Muminina (a.s) ya karantar da dansa Muhammad bn al-Hanafiyya yadda ake amfanuwa da ra’ayuyyukan ma’abuta hankali da kuma shawartarsu don isa ga hakika da abin da ya dace. Ya zo cikin wasiyyarsa (a.s) gare shi cewa: “Ka hada ra’ayoyin mutane waje guda, sai ka zabi wanda yafi kusanci ga hakika wanda kuma ya fi nisa daga rashin tabbas” har zuwa inda yake cewa: “ya sanya kansa cikin hatsari wanda ya wadatu da kansa, wanda ya karbi fuskokin ra’ayuyyuka ya fahimci wajen kuskure[37]”.

SiffofinWadanda Ake Neman Shawararsu

Saboda haka, tun farko yana da kyau mu san siffofin mutanen da ya kamata mu nemi shawarwarinsu da kuma yarda da ra’ayuyyukansu. Wadannan siffofi kuwa su ne kamar yadda aka ruwaito cikin ruwayoyin Ahlulbaiti (a.s) kamar haka:

1-     Riko da addini, tsantsaini, tsoron Allah.

2-     Ikhlasi yayin nasiha ta yadda zai kasance tamkar dan’uwa abin kauna ga mutumin da ya nemi shawarar tasa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next