Karfafa Ginin Al'ummaHaka nan an ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w.a) cikin wani hadisi yana cewa: “Ku sani cikin gaba akwai (aska) mai askewa, ba ina nufin mai aske gashi ba, face dai mai aske addini[23]â€. b)- wajibcin amsa sallama, haka nan wajibcin ba da amsa ga wasika ko takardar da aka aiko wa mutum da kuma kwadaitar da musanyan wasika maimakon ziyara da ganawa. An ruwaito Abu Abdullah (a.s) cewa: “Mayar da amsa ga wasikar (da aka aiko wa mutum) wajibi ne tamkar wajibcin amsa sallama, kuma wanda ya fara sallama shi ya fi cancanta a wajen Allah da ManzonSa[24]â€. Kuma yana cewa: “Ziyara ita ce sada zumunci tsakanin ‘yan’uwa a lokacin da ake gida, a yayin tafiya kuwa musayen wasiku[25]â€. c) – Kwadaitar da cika alkawari ko da kuwa bayan shekara ne. Abu Abdullah (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: duk wanda ya yi imani da Allah da Ranar Lahira, to ya cika alkawari idan ya dauka[26]â€. d) – Sanya sharudda ga abokin da ya cancanci yarda. An ruwaito daga Imam Sadik (a.s) fadinsa cewa: “Abokantaka tana da iyaka, duk wacce ba tada wadannan iyakoki, ba ta zama cikakkiyar abokantaka ba, haka nan wanda ba shi da wani abu na wadannan iyakoki ba za a sanya shi cikin abokantaka ba. Na farko sirri da abin da ya bayyana nasa su kasance abu guda a wajenka, na biyu ya dauki abin yabonka abin yabo, abin Allah wadai kuwa na Allah wadai, na uku kada kudi ko mulki ya canza shi daga gare ka, na hudu kada ya hana ka wani abin da zai iya baka shi, sannan na biyar kada ya guje maka yayin wahala[27]â€. e) – Abin da a nan gaba za mu ishara gare shi na hadiye fushi, mustahabbancin daidaita alaka ta yadda alakar ba za ta munana ba saboda gushewar kunya ko girmamawa ba. Ko kuma gargadi
|