Karfafa Ginin Al'umma



Ya zo cikin wata ruwaya cewa: “mai ba da shawara amintacce ne[47]”, kamar yadda aka ruwaito cikin wani hadisin daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Wanda ya nemi shawarar dan’uwansa amma sai ya ki ba shi shawara mai kyau (tsakaninsa da Allah), Allah Zai kwace masa ra’ayinsa[48]”.

Baya ga ikhlasi da ba da ra’ayi tsakani da Allah yayin ba da shawara, dole ne mai ba da shawara ya rufe asirin wanda ya nemi shawararsa saboda abin da ake nufi da ‘mai ba da shawara amintacce ne’ shi ne rufe sirri kamar yadda hakan shi ne ikhlasi, dukkan hakan shi ne abin nufi da amana.

Kamar yadda za a iya fahimtar hakan cikin cikin hadisin da ya gabata da ke cewa: “Na hudu ya kasance saninsa ga sirrinka tamkar saninka ne ga kanka, sannan kuma ya kula da kiyaye shi”.

Daga wadannan bayanai za mu iya fahimtar cewa batun neman shawara na daga cikin muhimman abubuwan da Ahlulbaiti (a.s) suka jaddada kansa yayin da suke magana kan alaka ta zamantakewa da ginin al’umma a yanayi na gaba daya.


[1] . Wasa’il al-Shi’a 11:567, Abwab Fi’il al-Ma’aruf, babi na 23, hadisi na 3.

[2] . Wasa’il al-Shi’a 11:567, Abwab Fi’il al-Ma’aruf, babi na 23, hadisi na 5.

[3] . Wasa’il al-Shi’a 11:568, Abwab Fi’il al-Ma’aruf, babi na 23, hadisi na 7.

[4] . Wasa’il al-Shi’a 11:568, Abwab Fi’il al-Ma’aruf, babi na 23, hadisi na 10.

[5] . Wasa’il al-Shi’a 8:410, Abwab Ahkam al-Ashra’, babi na 10, hadisi na 6.

[6] . Wasa’il al-Shi’a 8:432, Abwab Ahkam al-Ashra’, babi na 10, hadisi na 8.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next