Karfafa Ginin Al'umma



Babu shakka wannan tafarki na daga cikin muhimman tafarkin da ke karfafa alaka tsakanin mutane, da samar da karfafaffiyar ka’idar da ta ginu bisa asasin shu’uri da nauyi, yarda da fahimtar juna wajen isa ga hakikar da ake son isa gare ta.

Dole ne hakan ya tafi daidai da ka’idar hikima da wa’azi mai kyau.

Akwai nassosi masu yawa da suke magana kan hakan. A nan za mu yi ishara da wasu daga cikinsu:

Abu Abdullah (a.s) yana cewa: “Wajibi ne a kan mumini ya yi nasiha wa dan’uwansa mumini[7]”.

Kuma yana cewa: “Wajibi ne akan mumini ya yi wa dan’uwansa mumini nasiha a idonsa ko a bayansa[8]”.

Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: “Addini nasiha ne”, sai aka tambaye shi ga wa Ya Rasulallah? Sai ya ce: “Ga Allah, ga ManzonSa, ga imaman addini da sauran musulmi[9]”.

Daga Abil Udais yana cewa: Abu Ja’afar (a.s) ya ce: “Ya Salih! Ka bi wanda ke sa ka kuka alhali yana mai maka nasiha, ka da ka bi wanda ke saka dariya alhali yana mai cutar da kai, da sannu za ku koma wajen Allah gaba dayanku, sannan kuma za ku sani[10]”.

Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Mafi soyuwar ‘yan’uwana gare ni shi ne wanda ya yi min nuni da aibi na[11]”.

Kuma yana cewa: “Mumini ba ya wadatuwa da abu guda yana bukatuwa da abubuwa uku: mawafaka (dacewa) daga Allah Madaukakin Sarki, mai masa wa’azi da yarda da wanda ke masa nasiha[12]”.

Rahama,Tausayi da Ziyarce-Ziyarce Tsakanin Juna

Na uku: Umarni da rahama, tausayi da ziyarce-ziyarce tsakanin juna, saboda tausayi na daga cikin muhimman ababen da ke karfafa alaka da sanya ta bisa karfaffifiyar turba kamar yadda muka nuna a baya. Za a iya tabbatar da wadannan ababe ne a aikace ta hanyar wadannan kyawawan dabi’u.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next