Zabar Mace Ko Namijin Aure



4- Yin amfani da hanyoyin da zasu hana shi aikta haram da sha’awarsa kamar gaggauta yin aure da zaran ya samu dama; auren na da’imi ne ko kuma na mutu’a.

5- Tuna ni’imar da Allah yake bayar wa ga wanda ya bar sha’awarsa ya ki aikata haramun da ita, saboda Allah.

6- Sanin cewa wannan siffa ce ta dabbobi, shi kuwa mutum ne bai kamata ba ya zama kamar dabba domin shi an halicce shi ne domin kamala.

7- Ya yi duba da tunani da lura zuwa ga ayoyin kur’ani da ruwayoyi da suka kwadaitar da tuba, suka kuma zargi mai wannan hali[16].

8- Ya yawaita karatun kur’ani da karanta littattafai na ilimi na hikima, da yawaita addu’a, da jin cewa shi zai iya barin wannan hali, hada da matakan da muka ambata a sama.

Alkur’ani Da Dokokin Zamantakewar Aure

Ayoyin masu yawa ne suka zo a cikin littafi mai girma na kur’ani suna nuni zuwa ga dokokin zamantakewar aure da zamu kawo su a dunkule kamar haka:

1- Namiji shi ne shugaba a cikin iyali: Nisa’I:34.

2- Mace nutsuwar mijinta ce: Rum: 21.

3- Miji da mata tufafin juna ne: Bakara: 187.

4- Kyautata zaman tare da mata: Nisa’I: 19.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 next