Zabar Mace Ko Namijin Aure



Ga cikakkiyar ruwayar game da wannan al’amari tare da wasu karin bayanai:

Al’abi ya ce: A cikin littafin Nasruddurar: An rawaito daga Abdullahi dan Mu’ammar allaisi ya ce da Abi Ja’afar (A.S): Labari ya zo mini cewa kai kana bayar da fatawa da yin auren mutu’a? ya ce: Allah ya halatta ta a littafinsa kuma Manzo (S.A.W) ya sunnanta ta, sannan sahabbansa sun yi aiki da ita, sai Abdullah ya ce: Ai Umar ya hana yin ta. Sai imam Bakir ya ce: Kai kana kan maganar sahibinka, ni kuma ina kan maganar Manzon Allah (S.A.W). Sai Abdullah ya ce: Shin zai faranta maka rai (‘ya’yan) matanka su aikata haka? Sai Abu Ja’afar (imam Bakir) (A.S) ya ce: Kai wawa? Wannan da ya halatta ta a littafinsa kuma ya halatta ta ga bayinsa ya fi ka kishi da kai da wanda ya hana ta yana mai dora wa kansa nauyi, a yanzu zai faranta maka rai cewa ‘yarka tana karkashin auren wani masaki daga masakan garin Yasrib (Madina)? Sai ya ce: A’a. Sai imam (A.S) ya ce: Me yasa kake haramta abin da Allah ya halatta? Sai ya ce: Ba na haramtawa, amma dai masaki ba tsarana ba ne. Sai ya ce: Ai hakika Allah ya yarda da aikinsa ya so shi, ya aura masa Hurul-i’n, a yanzu kana kin wanda Allah yake son sa? kana kin wanda yake tsara na Hurul-i’n din aljanna saboda shisshigi da girman kai? Sai Abdullah ya yi dariya ya ce: Wallahi ba na ganin kirazanku sai mabubbugar ilimi, sai ‘ya’yan itacensa suka zama a hannunku, ganye ya rage a hannun mutane[23].

A littafin Khilaf na Shaikh dusi ya zo cewa; Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Muminai sashensu tsararrakin sashe ne, jini yana daidaito, mafi karantarsu yana kulla alkawarinsu[24].

Mas’ala 28: Ya halatta ga ajami ya yi aure da balarabiya, da bakuraishiya, da bahashima idan yana cikin ma’abota addini, kuma yana da yalwa.

Babu Dole Ko Tilasci A Aure

Musulunci ya hana auren dole[25], ya sanya shi kamar ba aure ba ne[26], don haka Uba ko Kaka na wajan uba duk da yana da hakkin yardarsa da izininsa a aurar da budurwa, amma idan zai yi mata auren dole da wani wanda ba ta kauna, a nan yarinya tana da iko ta yi aure da wanda take so matukar mumini ne kuma ba wani abu na tawayar Addini gareshi, wannan wani abu ne da musulunci ya tabbatar da shi, domin Allah ne ya ba shi hakkin walitakar, idan kuwa ya saba masa sai ya kwace izininsa. Amma bazawara, ko matar da ta cika hankali tana mai dogaro da kanta, ko kuma mai zaman kanta, idan zata yi aure, ita take da ikon aurar da kanta, babu wani mai iko a kanta sai wanda ta wakilta, haka ma namiji baligi shi ne yake da iko a kansa, shi ya sa a gun malaman mazhabar Ahlul Baiti (A.S) auren dole ba a lissafi da shi[27].

Al’amarin aure ba a sanya shi hannun waliyyai ba gaba daya kamar yadda ba a sanya shi a hannun ‘yan mata ba gaba daya, shari’a ta sanya shi shawara ne tsakanin waliyyai da ‘ya’yansu mata[28], amma maza samari su ne waliyyan kansu, sai dai idan sun wakilta wani.

Da wannan ne na kai ga sakamakon cewa, da al’ummarmu tana rayuwa ne bisa mahangar Ahlul Baiti (A.S), da ba a samu karuwai da yawa haka ba, har ma na kasance farkon wanda yake tausayin irin wadannan ‘yan mata -Allah ka shiryar mana da su- wanda a bisa binciken da na yi, mutane da dama sun shaida mini cewa, karuwai da yawa sun tabbatar masu da cewa, auren dole ne ya sanya su guduwa[29] kuma ya jefa su wannan hanya ta fasikanci. Ina ganin da wannan al’umma ta fahimci tafarkin kofar birnin Ilimin Annabi wato Sayyidi Ali (A.S), da ba mu samu kanmu cikin wannan yanayi mai muni haka ba, da Addini ya yi sauki ga mutane, domin da yawa abubuwa sun kuntata ne sakamakon tazara da aka samu da wancan tafarkin.

Don haka zabi ga ‘ya mace abu ne muhimmi, in ba haka ba in ta fashe, ta fi fashewar bom hatsari, domin mace ta fi namiji tausayi, don tana aiki da dabi’a sosai fiye da shi, amma in ta bushe, takan fi shi kekashewa, don tana iya hana danta da ta haifa nono, ko ma ta kashe shi, idan kana kokwanto tambayi kissar amare da suka sanya wa angwaye da abokanansu maganin bera a abinci ka sha labarai.

Wasu Daga Siffofin Abokin Zama

A nan zamu so mu yi nuni da wasu siffofi da suke munana da ba a son abokan zamantakewa namiji ne ko mace ya siffantu da su, kuma ana kin auren masu mafi yawa daga wadannan siffofi, kuma in an aure shi to ya kamata a tarbiyyatar da shi hanyar barin su domin samun damar gina al’umma ta gari, wadannan siffofi suna da yawa, amma ga wasu kadan daga ciki kamar haka:- Gori, Rashin kunya, kage, Rashin tausayi[30], Kausasawa kan juna da tausasawa ga waninsa, Zage-zage, Girman kai, karya, Masifa, Yawan bakin ciki da fushi, Mugunta[31], Kwadayin duniya[32], kazanta[33], Jahilcin da ba a shirye ake da nemna sani ba[34], Kasala[35], Fasikanci, da Miyagun dabi’u.

Saudayawa maza da ba su yi dace da mace ta gari ba suka zama ababan zalunta ko suka shiga wani mummunan hali, da yawa mata sun jawo wa mazajensu cutar ruhi, da fushi, da bugawar zuciya, da makamantansu, kuma abin da ya kamata mu sani shi ne, wadannan siffofi kamar yadda a kan samu mata da su haka ma maza sukan siffantu da su.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 next