Zabar Mace Ko Namijin Aurebarawon ya kasance yana furtawa da cewa ba abin da yanke hannun ya kara masa sai son Imam (A.S)[38]. Akwai kuma so na dabi’ar halitta na tausayawa da kauna, misalinsa shi ne irin so da kaunar da uwa da uba suke nuna wa ‘ya’ya ko kuma ‘ya’yan suke nuna wa iyayansu, akwai kuma so na dabi’a kamar son Ngozi da take kirista da wani musulmi yake yi mata ba don Addininta ba sai dai domin dabi’ar kyawunta, ga wanda yake son mace kada ya duba kyau na dabi’a kawai, ya kamata ya sa hankali ya duba so na farko wato imani da kyawawan dabi’u, wannan shi ne zai iya sanya shi ya cimma nasarar kafa gida na gari. Sandararren Tunani
Wani abokina ya taba ba ni wani labari na wani abu da ya faru a kasarsu a danginsu cewa: Wani daga danginsu ya nemi wata yarinya ita ma daga danginsu, da aka hana shi sai su biyun suka gudu suka je suna rayuwarsu cikin soyayya da kaunar juna, amma da aka gano inda suke, sai aka aika masa da cewa ya zo an yarda su yi aure, bayan aure, wata rana sai yake gaya masa cewa: Wannan abu yana ba shi haushi, lokacin da ya gudu da ita suna rayuwa ta jin dadi amma tun ranar da aka yi musu aure ta zama matarsa ta halal tun rannan sai ta canza masa fuska, idan ya shigo gida, irin murmushin da take yi masa a da yanzu babu shi, sai ta turbune fuska, ga jayayya a tsakaninsu, yanzu ta fita daga ransa har ma saboda rashin jin dadin zaman zai mata kishiya ne. Sai na ce da shi: Ai ta yiwu abin da ya sa take daure masa fuska ko murmushi babu don sun yi zaman banza ne kafin su yi aure, ko kuma ya dauka idan an yi aure zata rika yi masa wancan abin da take yi masa ne, kamar yadda muka kawo a farko ne cewa, wasu ‘yan mata sun dauka miji ba abokin rayuwar soyayya ba ne kamar yadda wasu samarin suka dauka. Wato idan aka gama samartaka aka yi aure sai batun soyayya da kauna ya kare, daga nan sai a fara rayuwa sandararriya busasshiya, domin da yawa daga matan sukan dauka sai karuwai da fasikai ne suke yin waccan rayuwar mai dadi da soyayya a tsakaninsu. Shi ya sa matan da suka jahilci ma’anar aure da wautarsu, saudayawa sukan tura mazansu wajan fasikanci wajan karuwai da matan banza, abin tambaya shi ne? Su matan banzan sun fi su sanin namiji ne ko kuwa? Ko kuma sun fi su Ilimin yadda ya kamata a kyautata wa namiji ne ko kuwa? Kusan su matan banza sun san yadda zasu ja hankalinsa amma ita wai ba ta sani ba, har ma wani lokaci wata da mijin ya shigo gida kamar ba ta san shi ba sai ta canza fuska, ko kuma ba ta ma san me za ta yi ta burge shi ko ta kyautata masa ba. Wato sai ka ga cewa ita karuwa ta iya yi wa farkanta wasa da dariya, amma da yawa daga mata su ba su san su yi wa mazajensu wannan ba, har ma wasu sun dauka sumbunta aiki ne na fasikan mata ga farkansu kamar yadda wata ta taba gaya wa mijinta sakamakon haka, tana mai cewa da shi: Kai je ba ni wuri ko an gaya maka ni karuwa ce. Wai an dauka sai da karuwa ne ake yin irin wannan? Ko ake tafiya kanti, da fak, da wajan shakatawa, da cinima, da wajan hutawa, da Gidan zu, da wajan shan askiran, da makamantansu. Tir! da tunanin da ya dauka rayuwa tana nufin iskanci da fasikanci ne. Wasu abubuwan ma an dauka yin su fasikanci da iskanci ne, saboda haka ba a ma tanadin su ta yadda zasu yi daidai da dabi’un musulunci da yanayin da kowa zai iya zuwa da iyalansa kamar cinima, shi ya sa ma ba a ma tanadar fim da waje da ya yi daidai da amfanar al’umma masu aure, har ya zama kowa yana da tunanin cewa da zai ga mata da mijinta a irin wadannan wurare sai ya dauka karuwa ce da farkanta. Ta haka ne al’adu marasa kyau suka sanya karuwai suka kwace wa mata da yawa mazaje, kuma ku bincika ku gani, mutanen da ke bin matan banza me suke nema, kuma yaya zamantakewarsu da matansu a rayuwar da suke yi tare? Koda yake ba duka ne haka ba, amma da yawa mutanen da karuwai suka kwace mazajensu saboda duk bangaren biyu ko daya daga cikinsu yana da sandararren tunani game da rayuwar zaman tare. Haka ma zaka ga wasu da dama daga muminai suna auren mutu’a sakamakon haka, dan kudin da suke samu maimakon ya sayo wa matarsa atamfa ko wani abu da zata amfana, sai ya ga matarsa ta mutu’a tana bukatar kudi sai ya ba ta, koda yake ba muna cewa hakan laifi ba ne shi a kan kansa. A bin mamaki gareku mata, ko me karuwa za ta nuna muku? Ko kuwa me take da shi ku ba ku da shi? Menene sauran mata suke da shi da ku ba ku da shi? Abin kunya da kuke bari su kwace miji kuna nan kuna bakin cikin da sai dai ya kara muku ciwo a zuci, yaya matan aure za su bari wannan al’umma tamu ta lalace! Ko ba su san gyaran al’ummar yana hannunsu ba ne?
|