Zabar Mace Ko Namijin Aure



4- Idan akwai lokutan da ya saba aikata wannan mummunan hali a cikinsu sai ya kirkiro wa kansa wani abu daban da zai shagaltar da shi a irin wadannan lokutan: kamar zuwa hawan sukuwar doki da sauransu.

5- Ya nisanci zama shi kadai har abada koda bacci zai yi to ya kasance cikin mutane, wato ta yadda idan ba wani abu na lalura ba kamar kama ruwa da bahaya to ba yadda za a yi ya kasance shi kadai.

6- Da zarar ya samu yalwa da dama to ya yi maza ya yi aure kada ya jinkirta ko kadan.

7- Raya karfin ruhinsa ta hanyar jin cewa zai iya maganin wannan halin da taimakon Allah.

8- Nisantar masu irin wannan hali nasa.

9- Cin abinci mai kyau da tsara lokutan cinsa, ta yadda ba kodayaushe ne zai ci wani abu ba, da kuma wanka da ruwan sanyi a wasu lokuta, da nisantar sanya tufafi masu matse masa jiki.

10- Addu’a da neman taimakon Allah, da jin cewa Allah yana ganin sa duk inda yake koda ya shiga daki ya rufe ne shi kadai, ya ji cewa kuma Allah zai yafe masa abin da ya yi, kuma ya daukar wa Allah alkawarin ba zai sake ba[7]

Wasu malamai sun kawo shi kamar haka:

1- Ya san cewa istimna’i yana daga zunubai da aka yi alkawari azaba ga mai yinsa[8].

2- Ya san cewa mutane zasu kyamace shi idan suka san yana yinsa[9].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 next