Zabar Mace Ko Namijin AureWasu mutanen kuwa mugwaye ne a gida, masu tsananta wa ga mata da yara, babu maganar so a irin wadannan gidaje har su da kansu ‘yan gidan ne sukan so ya yi nesa da gida saboda jafa’insa da kaushinsa kan iyalansa, ba maganar kalmar dariya da kwauna a fuskar nan, har ma akwai wanda ya yi sakaci da rashin lafiyar matarsa bai kula da ita ba har ta mutu, koda muka je kwasar kayan baiwar Allah nan gidan sai wari yake, ashe ta dade ba ta da lafiya! Haka nan ya bar ta babu kular kirki har ta mutu, Irin wadannan miyagun mutane ya kamata a bi hakkin dan Adam a kansu. Wani lokaci a kan samu azzalumi a ciki ita ce mace, a nan ba kasafai ake gane wa ba don kissar wasunsu, Irin wadannan mata sun fi kowa gana wa miji azaba, amma a waje, da wajan kawaye sun fi kowa hargowa da shewa, ana hira ana dariya, amma da ta ga mijin sai ta bata rai, har ma akwai mazan da suka zama kamar mahaukata ko kuma manyan fasikai masu bin matan banza saboda irin wadannan matsaloli da matan suka jefa su. Nasiha ta ga duka bangare biyun shi ne, mu ji tsoron Allah (S.W.T) mu gyara wannan al’umma tamu. Haka zaka ga wasu gidaje babu soyayya, ba dariya, sai bala’i da bakin ciki kai ka ce wadanda aka yi wa mutuwa, ba mai tausayin wani a ciki, idan ‘ya’ya sun taso sai su taso cikin fitina da rashin kwanciyar hankali da rigima, domin abin da suka koya kenan a gida. Shi ya sa Malaman tarbiyya suke ganin yana da kyau binciken yanayin gida kafin a auri ‘yar gidan. A irin wannan gida zaka ga ba soyayya, mai gida ya bar matar babu wani abin alheri da yakan yi mata don yana ganin kamar ya yi hasara ne, haka ma ita ba ta da tunanin ko kadan ta taimaka masa ko da wane abu na alheri ne. Nasihohinmu Gareku
Wannna wasu tattararrun nasihohi ne da zan ba masu son aure ko miji da mata domin zamansu da rayuwarsu su kyautata, da kuma gida wanda zai zama daya daga asasin gina al’umma ta gari. *Kada iyaye su yi wa ’ya’yansu auren dole. *Nisantar auran mai miyagun halaye kamar mashayin giya. * Shiryar da mumini ga wata mumina don ya aureta. *Ka yi aure don nutsuwa da kame kai, ko taimakon juna, ko gina al’umma ta gari. *Kada a tsananta aure ya yi wahala domin wani lokaci ana samun wannan wahalhalu ta hanyar al’adu ne ko rashin sanin ya kamata daga masu ikon zartarwa.
|