Zabar Mace Ko Namijin Aure



Zabar Mace Ko Namijin Aure

Hafiz Muhammad Sa’id

hfaza@yahoo.com

Kuma akwai daga ayoyinsa ya halitta muku matan aure daga kawukanku, domin ku nutsu zuwa gareta, kuma ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku, lalle a cikin wannan akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani.[1].

Gabatarwar Mawallafi

Ina godiya ga Allah da ya ba ni damar rubuta wannnan littafi mai suna “Zabar Mace Ko Namijin Aure” wanda yake nuni da wane namiji ko wace mace ce za a zaba don zama tare. Mun rubuta wannan littafi ne daidai yadda zai dace da al’adun mutanenmu da kuma bayaninsa bisa ra’ayoyi mabanbanta, wannan ya taso ne musamman bayan mun ga ya dace mu rubuta wani abu wanda zai zama mai amfani ga al’ummarmu.

Littafin ya kunshi takaitaccen bayani ne game da yadda ya kamata gida ya kasance, da siffofin ma’aurata, da kuma yadda ya kamata su kalli rayuwa, da abin da ya shafi kula da hakkin juna kamar yadda musulunci ya gindaya ba tare da ketare iyaka ba.

Muna fatan littafin ya zama mai amfani ga dan Adam a yanayin zamantakewar gida, ta yadda zai zama sanadi na gina al’umma saliha da cigaban duniyar musulmi baki daya.

Ina rokon Allah ya bayar da ladan rubuta wannan littafi ga malamaina da dukkan wanda ya sanar da ni wani abu da amfaninsa ya shafi duniya da lahira.

Hafiz Muhammad Kano Nigeria

hfazah@yahoo.com

Rabi’ul Awwl 1424 H.K

Khurdad 1382 H.SH

Mayu 2003. M



1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 next