Imamanci Da NassiAhlussunna suna ganin wannan mas’ala mai girma addini ya gafala ga barin ta a Kur’ani da Sunna, ya kuma dora nauyin yin hakan a kan al’umma da su zabi yadda suka so. Idan kuwa haka ne, muna iya tambaya cewa: Shin akwai wata ka’ida ayyananniya da al’umma zata iya dogara da ita wajan ayyana halifa? kuma yaya matsayinta yake a shari’a? Amsa: Sai suka ce: Akwai fuska uku ta ayyana halifa: Ta farko: Zabin shugabannin al’umma da ayyana jagoranta, wannan kuma ana cewa da shi tsarin shura. Sai dai tsarin shura bai dauki salo daya ba gun sahabbai, saboda haka sai suka samu sabani suka ce shura kala biyu ce: A-Tsarin shura na farko kamar yadda ya faru a bai’ar Abubakar da Ali dan Abi Dalib. B-Tsarin shura ta hanyar ayyana wasu adadi da halifan da ya rigaya ya yi, kamar yadda Umar ya yi. Ta biyu: Wasiyya: Ita ce halifa kafin ya mutu ya sanya wanda zai maye gurbinsa, kuma wannan ma ya dauki salo daban-daban har guda uku: A- Ya sanya halifa daya kamar yadda Abubakar ya yi a lokacinsa ga Umar. B- Ya sanya wasu jama’a da dayansu zai zama halifa kamar yadda Umar ya yi tsakanin mutane shida da zasu zabi halifa tsakaninsu. C- Ya sanya halifanci ga mutane biyu ko sama da haka ya kuma sanya ta mai bin juna kamar ya ce: Halifa bayana shi ne wane, idan ya mutu sai wane. A wannan tsari halifanci yana zama a jere kamar yadda ya tsara shi, kamar yadda Sulaiman dan Abdulmalik ya yi ga Umar dan Abdul’Aziz, sannan Yazid dan Abdulmalik bayansa, haka nan Haruna ya sanya ta ga ‘ya’yansa uku. Ta uku: Sa karfi, da mamaya, da kwace, da galaba da takobi: Ahmad dan Hanbal ya ce: Imamanci na wanda ya yi nasara ne[13]. A zahiri wannan nazarori gaba dayansu neman gyara kurakuran da wannan al’umma ta yi ne, domin wannan ba shi da wata madogara ko mahanga ta shari’a.
|