Imamanci Da NassiNa farko: Masu ganin sakamakon shawara ya zama dole ne ga shugaba ya yi riko da shi. Daga cikin wadannan akwai Muhammad Abduh da yake fada a bayanin ma’anar Ulul’amri da yake cewa: Ulul’amri su ne masu shugabantar al’umma a hukunci, kuma wannan su ne aka yi nuni da su a fadin Allah madaukaki: “Al’amarinsu shawara ne tsakaninsu†ba kuma zai yiwu ba shawara ta samu tsakanin dukkan al’umma, don haka ya zama dole a samu wasu jam’a masu wakiltar al’umma, da ba kowa ne ba su sai ma’abota girma da daukaka na wannan al’umma da aka yawaita ambatonsu, yana mai karawa da cewa: Wajibi ne a kan shugabanni su yi hukunci da abin da manyan al’umma suka zartarâ€[37]. Na biyu: Ra’ayin da yake ganin shawara a matsayin fuskantarwa kawai, babu wani kima da take da shi na shari’a a wajan tilasta shugaba ya yi riko da ita wajan zartar da abin aka hadu a kansa, ko kuma abin da mafi yawa suka tafi a kai. Daga cikin wadannan akwai Kurdabi, yayin da yake cewa a tafsirinsa “Shawara ta ginu ne a kan sabanin ra’ayoyi, mai shawara yana duba wadannan sabani ne, ya kuma duba wanda ya fi kusa da littafi da sunna in zai yiwu, idan Allah ya shiryar da shi zuwa ga abin da ya so sai ya yi niyyar aiki a kansa ya kuma zartar yana mai dogara gareshiâ€[38]. Amma malaman Shi'a sun tafi a kan ra’ayi na biyu a tafsirin ayar shura, Muhammad Jawad Balagi yana cewa: “Ka shawarce su a kan al’amari†ai ka nemi gyaransu, da kuma karkato zukatansu da shawara, ba wai domin zasu sanar da kai ilimin daidai ba ko sanar da kai ingantaccen ra’ayi ba, yaya kuwa zasu iya hakan alhali Allah (S.W.T) yana cewa: “Ba ya magana ta son rai, shi (al’amarin) ba komai ba ne face dai wahayi ne da aka yi†saboda haka idan ka yi niyya a kan abin da Allah ya umarce ka da hasken annabta ya kuma datar da kai a cikinsa sai ka aikata kana mai “ka dogara ga Allahâ€[39]. Shura a nazarin koyarwar Ahlul Baiti (A.S) tana nuna cewa ra’ayin musulmi ba ya lizimtar Annabi (S.A.W) yayin da madaukaki yake cewa: “Idan ka yi niyyar aiwatarwa sai ka dogara ga Allahâ€. Ashe kenan tsayuwa da aiki yana zama a bisa asasin niyyar Manzo (S.A.W) ba bisa abin da muminai suka yarda ba. Sannan shawararsa (S.A.W) ta kasance domin gane ra’ayin musulmi ne ga yadda za a zartar da hukunce-hukuncen musulunci, ita shawarar ba a matsayin fitar da hukuncin shari’a take ba, hada da cewa Ubangiji madaukaki ya ce: “Bai kamata ba ga mumini ko mimina idan Allah ya hukunta wani al’amari ya zama suna da zabi a al’amarinsu, duk wanda ya saba wa Allah da manzonsa hakika ya bace bata bayyananneâ€[40], Ashe kenan rinjayar da shawara yana takaita da wajan da Allah da manzonsa ba su yi wani hukunci ba ne, amma abin da suka yi hukunci a ciki, shawara a nan sabo ce ga Allah da manzonsa da kuma bata bayyananne[41]. Saboda haka shura tana da kima ne idan ta amfana wajan daukar dokokin zartarwa na musulunci a dukkan fagagen rayuwa da makamancinta, kuma ba ta zama dole ga imami ma’asumi ba, domin ita ba ta iya shar’anta hukunci sabanin magana da zance da tabbatarwar ma’sumi, tana kebanta ne da wajan da Allah da manzonsa ba su da hukunci. Amma ta bangaren tarihi kamar yadda muka ambata shura ba ta zama wani tsari na siyasa na shari’a na hukunci ba, domin an kirkiri ra’ayinta ne domin gyara barna da kuskure na tarihi da kuma sanya wannan a matsayin madogarar asasi ta tarihi a tsarin shugabanci na wannan lokaci, kuma mu sani halifanci ba ya tabbata sai da nassi daga Annabi ga halifan da zai zo bayansa. Alaka Tsakanin Bai’a Da Nassi
Bai’a girmamawa ce ga mutum domin ya zabi makomarsa a cikin kira zuwa ga Allah da jihadi a tafarkinsa ko sha’anin hukunci da siyasa. A bisa dabi’a muslunci ba ya son rayuwar musulmi ta kasance ba tare da nufinsu ba da kuma yardarsu ba. Biyayya a nan ita ce mafi muhimmnaci a cikin zartar da ayyukan isar da sako da kira, da kuma ayyukan kasa, da jihadi, da karfafa wa ga bin imamai ma’asumai ta hanyar bai’a. Amma wannan ba yana nufin biyayya ga imami ma’asumi tana saraya ba ne idan ba a yi masa bai’a ba.
|