Imamanci Da Nassi



Shahidus sani a risalarsa: Asasi na hudu shi ne gaskatawa da imamancin imamai sha biyu (A.S), wannan asasi jama’ar imamiyya su na la’akari da shi wajan tabbatar imani, har ma ya zama wani larura daga larurai na mazhabarsu sabanin wasunsu na daga masu saba musu, su sun dauki wannan a matsayin furu’a ne[11].

Saboda haka ne zamu samu cewa, al’amarin ayyana imamai yana wajen hakkin dan Adam ne, kuma ba zai iya zabar wanda yake da isma ba, ko kuma ya gano wanda yake da ilmi na baiwa daga Allah da sauran siffofin da imamai (A.S) suke dauke da su.

Rashin kasanewar zabin imamai ta hanyar dan Adam ya yi kama da zabin annabawa da Allah yake zabar wanda ya so, kuma a gane hakan ta hanyar wahayi da nassi. Bambanci tsakanin Annabi da imami shi ne, Allah yana nuna Annabi ta hanyar mu’ujiza da wahayi, imamai kuma ta hanyar mu’ujiza da nassi.

Sharif Murtada yana fadi a risalarsa cikin abin da yake wajibi a kudurce shi game da annabta: Duk sadda Allah madaukaki ya san akwai maslaha a cikin wasu daga ayyukanmu da tausasawarsa, ko kuma akwai fasadi da barna na addini a ciki, kuma hankali ba ya iya gano ta, wajibi ne ya aiko Annabi domin ya sanar da wannan ga mutane, kuma babu wata hanyar gano shi sai da mu’ujiza. Mu’ujiza kuma dole ta kasance ta saba wa al’ada, kuma ta yi daidai da da’awar Manzo din da abin da ya shafi da’awarsa, ta kuma kasance ba za a iya zuwa da ita ba ta bangaren wani mutum, kuma aikin ya zama ya yi daidai da yadda Allah (S.W.T) ya gudanar da shi, idan wannan duk ya faru to wajibi ne a gaskata shi, in ba haka ba to sai rashin gaskata shi ya zamanto ya munana.

Daga abin da ya zo a babin abin da ya wajaba a kudurce shi a imamanci da kuma abin da ya biyo bayansa, ya wajabta kasancewar imami ya zama ma’asumi, domin da bai zama hakan ba, da bukatuwa a gareshi ba ta kare ba, wannan kuma yana tukewa zuwa ga samar da shugaba ma’asumi, kuma wajibi ne ya zama mafificin al’umarsa, mafi saninta, saboda munin gabatar da wanda aka fi a kan wanda ya fi shi a hankalce, Idan ya wajaba ya zama ma’asumi to wajibi ne a samu nassi daga Allah a kan hakan, kuma zabar imamanci ta bangaren mutane ya kawu kenan, domin babu wata hanya da mutane zasu iya sanin mai isma[12].

Don haka ne zamu samu nassi da yake daya daga rukunan isma a mahangar Shi’a da yake nuna ajiya ta Ubangiji da take tattare da wannan imami, daga nan ne zamu sami cewa nassi shi ne mai kai wa ga sanin halifa mai bin Manzo (S.A.W) a wannan aiki na addini da ci gabansa.

Nazarin Nassi Da Shura

Idan mahangar musulunci ga halifanci bayan mazo (S.A.W) ta lizimta samuwar nassi da wannan nazari yake gani bayan wucewar Manzo mai tsira da aminci, wanda ya wuce maganar jagoranci na siyasa, ashe kenan menene matsayin musulunci game da shura da wasu mutane suka lizimce ta a matsayin nazari ga shugabancin al’umma maimakon nassi? Kuma menene alakar shura da tabbatar da immanci da ake da nassi game da shi?

Zamu bi wannan mas’ala ta fuskacin tarihi da farko, sannan sai mu bujuro da nassi kan halifancin Annabi (S.A.W), bayan haka sai mu yi bincike game da dokokin shura da kuma alakarta da shugabanci da aka yi nassi da shi, domin mu kai ga natija zuwa ga cewa shura ba kawai nazari ne na hukuncin musulunci ba, sai dai wani abu ne na fakewa da shi da ake amfani da shi wajan nuna wadatuwa ga barin shari’ar musulunci, da daukar wata hanya da ta saba mata da take fitar da dokoki da ba su yi daidai da abin da ma’asumi yake a kai ba. Kuma shura ba wani abu ba ne a musulunci sai hanya ce da aka samu domin gyara abin da ya faru na kuskure a tarihin musulunci, da kuma neman ba shi mazauni a cikin shari’ar musulunci, wato ana iya cewa hanya ce ta halatta kuskure da gyara shi, da ba shi mafita da uzuri, ba nazari ba ce da shari’a ta zo da ita ba.

Na Farko: Ta Fuskacin Tarihi

Sanannen abu shi ne musulunci bai bar al’umma haka nan babu fikira game da hukunci ba, domin al’amarin addini da duniya gaba daya ba ya cika sai da samuwar shugaba da zai jagoranci al’umma, yana shiryar da ita, yana jagorantarta ga abin da yake gyara ga rayuwar al’umma da makomarta.

Saboda haka suka ce: Musulunci ya bar al’umma ta zaba wa kanta hanyar hukunci da kuma abin da take gani shi ne mafi maslaha ga kiyaye tsarinta da kuma kare shari’a, wannan kuwa ba yana nufin ya bar ta haka nan ba. Saboda haka wani ra’ayi ya bayyana a tarihin musulunci yana mai jingina al’amarin hukunci da jagoranci daidai da abin da ya faru a tarihi a lokacin sahabbai.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next