Imamanci Da Nassi



Wannan mutum yana dauke da siffofi madaukaka ta wata fuskar, da kuma siffar karkata zuwa ga kaskanci a gefe guda, abin da yake nuna cewa shi abin halitta ne daya da yake mallakar nufi da ‘yanci a kan ya zabi aiki mafi karfi da kuma matakin da ya dace domin gina rayuwarsa.

An ba wa mutum wannan ne domin ba shi damar motsawa a dukkan sasanni mafi fadi da yake keta duniyar mariskai zuwa sama da hakan, da kuma nuna cewa samuwarsa tana da wani hadafi da hannun kudura ya zana shi. Ba a halicce shi don wasa ba, ba a kuma bar shi haka nan ba, kamar yadda ambato mai hikima ya fada yayin da ya ce: “Shin kuna tsammanin mun halicce ku don wasa, kuma ku ba masu komowa ne zuwa garemu ba[5]”.

Kokari a cikin wannan hadafi da tsari da aka shirya su domin kaiwa ga hadafin asasi bai takaita da dan Adam ba, akwai sauran halittu da suke tarayya da shi a wani bangare da nassin Kur’ani mai girma yake cewa: “Ba mu halicci sammai da kasa da abin da yake tsakaninsu ba muna masu wasa[6]”. Idan ya tabbata cewa halitta dukkanta tana tafiya da hikima, da tafiyarwar Ubangiji wacce ta hada da mutum, kuma dukkansu masu tafiya ne zuwa ga cimma wani hadifi da ake bukata, kuma cewa kowane abu yana da shiriyarsa, to menene hadafin da saboda shi ne aka halicci mutum?

Kur’ani mai girma yana iyakance wannan hadafin da aka halicci mutum saboda shi da fadinsa: “Ban halicci mutum da aljani ba sai don su bauta mini[7]”. A nan zamu yi la’akari da cewa kalmar taskacewa da togewa (sai don) tana nufin Allah ba shi da wani hadafi da manufa na halittar mutum sai ibada, kalmar don su bauta min tana bayanin sababi da dalilin halitta shi ne, wato mutum halitta ce don ibada ga Allah, Amma tambaya a nan ita ce: Idan hadafin halittar mutum yana takaituwa ne a ibada ba wani abu ba to mecece ibada? Menene kuma hakikaninta?

Idan hadafi na karshe na halittar mutum shi ne kusancin Allah da bauta da dan Adam yake samun kamala da ita, to menene yake tunkuda shi domin kaiwa zuwa ga wannan kamalar?

Hakika mutum a dabi’arsa da fidirarsa yana riskar cewa, biyan bukatarsa tana zama ta hanyar da zai iya toshe tawayar da take samunsa, kamar yadda yake riskar bukatarsa ta hanyar abubuwan da sukan iya kai shi ga kamalarsa sai ya motsa domin nemanta, sai dai tambaya a nan ita ce: Ta yaya ne zai kai ga wannan kamalar?

Daga nan ne zamu samu hikima ta Ubangiji ta hukumta sanya wa mutum abubuwan da ta hanyar su ne zai iya sani da tarbiyya da rikon hannunsa zuwa ga kamala. Yayin da abubuwan da dan Adam yake riska shi kadai da hankalinsa suka zama sun gajiya a kan su kama hannun shi wannan mutum domin su kai shi zuwa ga tafarkin tsira koda kuwa ya nemi taimakekeniya da dan’uwansa mutum, domin mafi nisan abin da dan Adam yake mallaka shi ne taimakekeniya don fahimtar gaskiya da hakika a iyakar fagen hankali da mariskai, alhalin wadannan fagage biyu ba su isa ba ga riskar hakikanin gaskiya da zata kai ga kamala.

Saboda haka ne hannun gaibi (Taimakon Ubangiji) ya miko domin toshe bukatar mutum wacce take ita ce mafi girman bukatarsa, sai mutum na farko ya zama dan aike daga Allah kuma mai shiryarwa zuwa ga tafarki madaidaici.

Aikin annabawa ga mutane shi ne bayanin ilmi, da kyawawan dabi’u, da sanin gaskiya da zata kai ga kamala da tarbiyya mai kyau, da kuma bayanin ilmi da dan Adam zai iya fahimta, da kuma bukatuwarsa zuwa gareshi, sai dai shi ba ya iya kai wa ga hakikaninsu ta hanyar lalatacciyar tarbiyya, ko kuma mutum yana bukatar lokaci mai tsawo kafin ya kai ga gano su wadannan ilimomi, kamar sunnar Allah ta halakar da dan Adam sakamakon kaucewa gaskiya da kin ta, ko sunnar Allah a kan cewa abin da mutum ya zaba da sannu zai kai shi ga sa’ada da kamala, sai dai shi ne yake barin ta saboda karkatarsa zuwa ga duniya.

Sai muhimmancin aiko Annabi ya bayyana a nan domin ya tunatar, ya yi gargadi. Ubangiji mai girma ya ce: “Ka tunatar domin kai mai tunatarwa ne kawai[8]”. Kamar yadda muhimmancin Annabi yake bayyana da wajabcin samar da shi da la’akari da cewa, shi yana misalta jagoranci ne na aiki na gari, domin shi mutum ne cikakke a ayyukansa da dabi’arsa da kuma sadaukarwarsa, wannan shi ne abin da ake cewa da shi muhimmancin tsarkake rai.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next