Imamanci Da NassiSakamakon ra’ayinsu game da imamanci da halifanci wani abu ne da bai wuce jagoranci na siyasa ba, kuma haka ya isa ya kasance ta hanyar zabe da shura, da kwace da karfi, da gado, ko wasiyya, kamar yadda yake a bayyane a aikace na ayyuka masu rikitarwa da suka faru bayan wafatin Manzo (S.A.W) da sharadin adalci, da ilimi daidai gwargwado. Saboda haka ne wasu suke tambayar larurar samuwar imami boyayye, ko kuma larurar ya zama ma’asumi, ko larurar ayyana shi da nassi daga manzon Allah (S.A.W). Amma koyarwar Shi’a tana cewa ne, imamanci da halifanci bayan Manzo (S.A.W) abu ne mai girma na Ubangiji tamkar muhimmancin aiko da Manzo, kuma mai cigaba ce har karshen duniya, sai suka shardanta isma a cikinta hatta kafin balaga, hade da ilimi da yake daga Allah, da kuma nassi na shari’a ga imami. Saboda haka makarantar Sunna ba ta ganin wadannan sharudda da wata ma’ana da kima, kuma ba sa ganin sun dace da aikin da halifa zai yi, sharudda a nan gun mazhabin Ahlul Baiti (A.S) sun wuce na muhimmancin aikin siyasa kawai. Wannan shi ne mataki na farko, kuma wajan sabani da yake fassara mana sabanin da ake da shi a fahimtar imamanci da kuma kokwanto a mas’alar isma, ko kuma dalili na wajabcin samuwar nassi. Wannan shi ne ya sanya wasu suka yi bincike game asalin nazarin samun nassi domin su kai ga natija zuwa ga cewa; babu wani tarihin da ya nuna hakan a rayuwar imamai. Wannan batun da aka tayar game da imamanci da halifanci da nazarin nassi da kokwanto game da hakan, ya faru ne sakamkon fahimta da Ahlussunna suka yi wa imamanci. Sai dai magana ingantacciya ita ce; imamanci a Kur’ani da Sunna sun wuce wannan fahimta, kuma ta saba gaba daya daga asasinta daga irin wannan fahimta maras zurfi ta ma’anar imamanci da jagorancin al’umma bayan Annabi. Koyarwar Ahlul Baiti (A.S) tana kudurce cewa imamai goma sha biyu suna da muhimmiyar rawar da suka taka da ta lizimta sharudda masu zurfi mafi tsanani daga sharuddan jagoranci na siyasa[10]. Alaka Tsakanin Isma Da Nassi
Idan aikin imami shi ne makoma na addini, kuma aikinsa a shari’ance yana mikuwa zuwa ga sasanni masu yawa da ya hada da akida, da hukuncin shari’a, da kyawawan dabi’u, da jagoranci, kuma wajibi ne binsa da karba daga gareshi, saboda haka zantuttukan imami ma’asumi da ayyukansa, da abin da ya tabbatar duk hujja ne na shari’a da take hawa kan baligi a wajabci ko uzuri ga wanda bai sani ba daidai da hujjar ayyukan Manzo (S.A.W). Wannan aiki mai girma yana lizimtar abubuwa da yawa kamar haka; Imami ya zama ma’asumi kamar ismar Manzo, da wajabci a kansa na isar da sako kuma da aiki, wannan yana bayyana cewa isma da wannan ma’ana ba sharadi ba ce ga aikin jagoranci na siyasa kawai. Muhimmancin aikin imamanci ya wajabta kasantuwar imami ya zama masani da dukkan abin da al’umma take bukata zuwa gareshi na rayuwarta da makomarta, kuma dole ya zama mafifici daga duk wanda yake bayan kasa a zamaninsa domin ya samu bayar da hakkin wannan aiki mai nauyi. Shi’a suna da imani cewa Manzo (S.A.W) ba shi da kansa ne ya ayyana halifa ba, sai dai al’amari ne da Allah ya umarce shi da shi, domin hadafin imamanci da kuma al’amarinta ya doru a kan al’amarin cikar sakon annabci da kuma cigaban shiriyar Ubangiji a kan layi daya. Hikimar Allah ta sanya cigaban isar da sakon Allah ya zama ta hanyar ayyana imami ma’asumi ne, imami shi ne wanda ya lamunce samar da maslaha ta tilas ga al’ummar musulmi bayan Manzo (S.A.W). Ashe kenan matsayin imamanci na akida ba kamar fikihu ba ne na daga hukuncin rassa, wannan shi ne abin da ya sanya imamanci ya zama yana da wadannan sharudda masu fadi masu girma, kuma ya wuce matsayin jagoranci na siyasa kawai. Idan muhimmancin imamanci yana da fadin da ya wuce jagorancin siyasa to dole ne ya zama yana da sharadi da zai tilasta gaskatawa da shi a matsayin wani asasi na addini kai tsaye, saboda abin da yake mai girma na sakon da yake dauke da shi.
|