Matasa Da RayuwaKamar yadda kuma yana da kyau mu dinga amfani da kwarewar da wasu suka samu kan wannan abu da kuma shawartar wadanda muka yarda da su; kamar uba, uwa, dan'uwa, abokai, malamanmu, kwararru kan lamarin da dai sauransu. Akwai abubuwa da dama da suke motsa dan'-Adam zuwa ga fushi, kiyayya, son kai, aikata laifi da kuma sanya kai cikin ayyukan da ba zai iya tsira daga mummunan sakamakonsu ba. Tana iya yiwuwa wahami da kuma rashin tabbaci su auri mutum, ta yadda zai dinga kitsa wasu abubuwa da ba za su iya tabbatuwa ba ko kuma burace-burace don cimma biyan bukatan sha'awarsa, da suka hada da son dukiya, ko kuma shahara ko kuma wani matsayi da dai makamantan hakan. Don haka sai ya bata lokaci da dukiyarsa ba tare da ya samu wannan abu da yake burin samu ba, face ma dai dukkan wadannan abubuwa su tafi a banza. Kana kuma tana yiwuwa sha'awa da kuma burace-buracensa na son jin dadi su sanya shi sabawa da wasu munanan dabi'u, kamar shan muggan kwayoyi, taba, zinace-zinace da sauran ayyukan da za su sanya shi cikin nadama da bala'i, ta yadda ba zai taba fahimtar haka ba sai bayan da lokaci ya kure. Hakika yana daga cikin hikima da kuma sanin ya kamata kar mutum ya sake aikata kuskuren da ya riga ya aikata kuma ya ga sakamakonsa, kamar yadda kuma ya kasance yana daga cikin hikima kada mutum ya aikata kuskuren da waninsa ya aikata....lalle kwarewar makaranta tana koyar da mutum isa ga manufa da kuma yin kuskure. Don haka ya hau kansa ya yi amfani da kuskurensa da kuma kuskuren sauran mutane don gyara kansa da kuma tsira daga fadawa cikin kuskure. Masu iya magana suna cewa: "Wanda ya jarraba abubuwan jarrabawa, to ya tsira daga nadama". Imam Ali (a.s.) yana ce wa: "Mai samun rabo shi ne wanda ya wa'aztu da waninsa"([1]) . Girmama Halin Mutum:
Hakika mafi girman da kuma daukakan abin da mutum zai iya mallaka a rayuwarsa shi ne hali da kuma mutumcin kansa, hakan kuwa wata amana ce da take a kan wuyansa wacce Allah Madaukakin Sarki Ya daukaka shi da ita. Sannan kuma Ya haramta masa ha'intar kansa ko kuma kaskantar da ita da kuma ha'intar abin da Ya ba shi na kwarewa.
|