Matasa Da RayuwaLalle yana da kyau ko wane daya daga cikinmu ya yi tunani yayin da yake karanta wannan hakika na ilimi, ya tambayi kansa ya ya aka yi aka sami irin wannan tsarin....kuma Wane ne Ya sana'anta hakan? Hakika Alkur'ani mai girma ya amsa mana wannan tambaya, yayin da yake ce wa: "....bisa sana'ar Allah Wanda Ya kyautata kowane abu....". (Surar Namli, 27: 88) "Shi ne Wanda Ya halitta sammai bakwai, dabakoki a kan juna, ba za ka ga goggociya ba a cikin halittar Allah Mai rahama...." (Surar Mulk, 67: 3) "Kuma rana tana gudana zuwa ga wani matab-baci nata. Wanda kaddarawar Mabuwayi ne, Masani. Kuma da wata, Mun kaddara masa man-ziloli, har ya koma kamar tsumajiyar murlin dabino, wadda ta tsufa. Rana ba ya kamata a gare ta, ta riski wata. Kuma dare ba ya kamata a gare shi ya zama mai tsere wa yini, kuma dukkansu a cikin sarari guda suke yin iyo". (Surar Yasin, 36: 38-40) To idan wannan ita ce duniyar kasa da sama, bari mu koma ga kogi da kuma abubuwan da suka kewaye mu. Lalle wani irin kyau ne wannan duniya take da shi, duniyar da take cike da dabbobi, kifaye, lu'u-lu'u da murjani...... Hakika bincike da karatuttukan da kwararrun malami suka gudanar sun kai su ga gano abubuwan ban mamaki na wannan duniya....abubuwan da suke sanya mutum cikin tunani da mamakin girman wadannan sirrori da suke tattare da wadannan halittu na cikin ruwa. Wannan sanannen malami (Karisi Maurisun) cikin wannan littafi nasa mai suna "al-Ilmu Yad'uw lil-Iman" ya nakalto mana wani labari dangane da kifin salmon da kuma macijin ruwa, inda yake bayyana cewa: "Bayan binciken da suka yi kan wadannan kifaye, malamai sun gano abubuwa masu ban al'ajabi kwarai. Wadannan kifaye su kan haihu a cikin kogi, amma sai su tafi su rayu na shekaru cikin teku, sannan daga baya su dawo cikin kogin da aka haife su. Kuma idan aka dauko su daga wannan kogi zuwa wani kogi na daban wanda suke hade, za su dinga iyo har sai sun koma cikin kogin da aka haife su.
|