Matasa Da Rayuwa



Hakika Mahaliccin rayuwa Ya bai wa mutum ita (rayuwa) ce don ya rayu cikin kwanciyar hankali da jin dadin abubuwan jin dadin cikinta da kuma kawaice-kawaicenta, gwargwadon yadda dokokin kiyaye rayuwa da kuma kyautata dabi'u suka tanadar. Ta yadda zai iya tabbatar da alheri a kansa da kuma al'umma da yake rayuwa a cikinta....

Babu shakka, a lokacin da mutum ya yi kuskuren fahimtar rayuwa, to lalle zai cuci rayuwarsa da kuma ja-gorantarta zuwa ga halaka, kuma da wuya ya iya gane wannan kuskure na sa sai bayan gushewar lokaci.

Don da yawa daga cikin mutane, sha'awoyi, son zuciyarsu da kuma gururi sun kai su zuwa ga halaka da kuma nadama, hakan kuwa bayan kurewar lokaci..

Rayuwar irin wadannan mutane ta kare a gidajen yari daban-daban, kashe kai, kamuwa da muggan cututtukan jima'i (irinsu ciwon AIDS da dai sauransu), shan muggan kwayoyi, damuwa, tabewa da dai sauransu.

Cibiyoyin kididdiga da bincike irin su asibitoci, cibiyoyin lafiya da kuma na muggan laifuffuka sun tabbatar da adadi mai yawan gaske na faruwar irin wadannan laifuffuka a tsakanin al'umma....

Hakika rayuwarmu kyauta ce ta Ubangiji Mai rahama, don haka dole ne mu yi mu'amala da rayuwarmu daidai da dokokin kiyaye lafiya da kuma rayuwa. Hakan kuwa su ne dokokin Ubangiji, Wanda Ya haramta mana duk wani abin da zai cutar da mu, sannan kuma ya halalta mana dukkan alherori da jin dadin da suke da amfani a gare mu....

Akwai hanyoyi na fahimtar rayuwa, don haka wajibi ne mu koma gare su da kuma dogaro da su. Wadannan hanyoyi kuwa su ne:

1.  Littafin Allah da kuma shiryarwar Annabci; wadannan abubuwa guda biyu suna mana cikkakken bayanin rayuwa da kuma hanyoyi da tafarkin shiriya cikin rayuwarmu. Don haka dole ne mu karanta su tare da tunani da kuma cikakkiyar fahimta, don mu san abin da ke cikinsu na alheri da kuma hikima.

2.  Mabubbuga ta biyu na fahimtar rayuwa shi ne ilimi da bincike-bincikensa. Hakika ilimi ya arzurta mu da masaniya da kuma fahimta, ta yadda ya iya bayyana mana abubuwa masu cutarwa da kuwa masu amfanarwa. Sannan kuma wadannan abubuwa da ilimi ya tabbatar da su sai suka yi dai-dai da abin da Alkur'ani mai girma ya tabbatar na haram da halal....

Hakika ilimi ya gano hadarin da ke tattare da giya, muggan kwayoyi, zinace-zinace, cin kudin ruwa, haka nan kuma ya gano fa'idar tsabta, soyayya, sada zumunci tsakanin 'yan'uwa da kuma tasirin da yake da shi wajen kiyaye zaman lafiyan al'umma, da kuma tasirin imani wajen sa'adar dan'Adam, tabbatuwa cikin dabi'u na kwarai, tsira daga damuwa da kuma muggan laifuffuka.....da dai sauransu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next