Matasa Da RayuwaSannan kuma yana daga cikin hakkin dan'Adam ya rayu cikin tsaro da kwanciyar hankali, shi da dukiyarsa da kuma dukkan abin da ya mallaka, hana shi wannan 'yanci kuwa zalunci da babakere ne wanda mai aikata hakan ya cancanci azaba. Kana kuma kamar yadda hakan ya zamanto 'yancinsa, haka nan ma ya zamanto 'yancin wasunsa ne....don haka a duk lokacin da ya yi wasa da tsaron lafiyar wasunsa, ko kuma ya aikata wani abin da zai tsoratar da su, ko kuma ya haifar da rashin tabbas da kwanciyar hankali a cikin mutane, to ba makawa ya zamanto abokin gaban al'umma, kuma hakan ma wasa ne da tsaron kan kansa shi ma. Manzon Allah (s.a.w.a.) ya tabbatar da ka'idar tsaro da kwanciyar hankalin al'umma cikin fadinsa cewa: "Musulmi dan'uwan musulmi ne, don haka kada ya cutar da shi, ko ha'intarsa ko ya fadi mummunar magana dangane da shi. Sannan kuma jininsa ba ya halalta a gare shi, haka ma dukiyarsa sai da yardarsa([5])". Daraja da daukakar dan'Adam tana ga mutumci da karamarsa ne, don haka shari'ar Musulunci ta haramta giba, bata suna, yada kararraki da zubar da mutumcin mutum ta hanyar magana ko aiki ko kuma ta hanyar bincike da bayyana asirin mutum da dai sauransu. Wannan doka ta Musulunci tana wajabta wa mutum girmama mutumcin sauran mutane, kan kuma ba ya halalta ya keta hurumin sauran mutane.... Allah Madaukakin Sarki Yana ce wa:
"Ya ku wadanda suka yi imani! Kada wadansu mutane su yi izgili game da wadansu mutane, mai yiwuwa ne (abin yi wa izgilin) su kasance mafifita daga gare su (masu izgilin), kuma wadansu mata kada su yi izgili game da wadansu mata mai yiwu-wa ne su kasance mafifita daga gare su. Kuma kada ku aibanta kanku, kuma kada ku jefi juna da miyagun sunaye na lakabobi. Tir da suna na fasicci a bayan imani. Kuma wanda bai tuba ba, to, wadannan su ne azzalumai. Ya ku wadanda suka yi imani! Ku nisanci abu mai yawa na zato. Lalle sashen zato laifi ne. kuma kada ku yi rahoto, kuma kada sashenku ya yi gibar sashe. Shin dayanku na son ya ci naman dan'uwansa yana matacce? To, kun ki shi (cin naman). Kuma ku bi Allah da takawa. Lalle Allah Mai karbar tuba ne, Mai jin kai". (Surar Hujurat, 49: 11-12) Haka nan kuma mutum yana da wasu hakkoki a kan al'umma da kuma kasarsa, wadanda gwam-nati ce take daukan mafiya yawa daga cikinsu; wadannan hakkoki sun hada da bayar da ilimi, tarbiyya, kula da samar da tsaro, kiwon lafiya da dai sauransu.... Kamar yadda kuma kasa da al'umma suke da wasu hakkoki a kan mutum, kamar su kiyaye maslahohin al'umma da kuma kare su, bugu da kari kan wajiban da suka hau kansa wadanda doka ta yi bayaninsu, wadanda matukar dai bai kula da kuma kiyaye su ba, to rayuwar al'umma za ta kasance tana fuskantar matsaloli da kuma rugujewa. A irin wannan hali shi ma ba zai tsira daga bala'in da zai fada wa sauran al'umma ba.
|
back | 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 | next |