Matasa Da Rayuwa"Wata rana Abu Abdullah ya ce min, a lokacin kuwa farashin kayayyaki ya tashi a garin Madina,: ya ya yawan abincin da muke da shi?, sai na ce masa: muna da abin da zai ishe mu na tsawon watanni. Sai ya ce: Fitar da shi ka sayar wa mutane, sai na ce masa: babu abinci a garin Madina fa. Sai ya ce: ka sayar dai, to lokacin da na sayar, sai ya ce min: je ka dinga saya tare da mutane rana-rana. Sai Imam Sadik ya ce: Ya Mu'attab, ka sanya abinci iyalaina ya zamanto rabi sha'iri rabin kuwa alkama, hakika Allah Ya san cewa ina da karfin ciyar da iyalaina da alkama, to amma ina son Allah Ya gan ni ina kyautata rayuwa gwargwadon bukatata([4])". Wannan kissa tana nuna mana irin yadda Musulunci yake ba da muhimmanci a aikace ga al'amurran da suka shafi al'umma. Don Imam Sadik (a.s.) ya ki yarda ya ajiye abincin da zai ci na watanni ga iyalinsa, a daidai lokacin da sauran al'umma suke cikin rashi da kuma kuncin abin da za su ci na rana guda. Kana kuma ya aikata hakan ne don wanda yake da karfin sayan abinci da yawa ya tara a gidansa ya nesance yin hakan don a samu kayayyakin abincin a kasuwa da yawa, ta yadda kudinsu za su sauko kasa kuma marasa karfi su sami daman saya. A nan za mu ga ce wa Imam Sadik (a.s.), kamar yadda ya ba da muhimmanci ga al'amarin al'umma, to haka ma a bangare guda ya bai wa lamarin kula da iyalansa nasa muhimmancin shi ma. To wannan shi ne cikakken imani na gaskiya. A nan yana da kyau a fahimci cewa, abu mai wahalar gaske ga mutumin da ya cutar da al'umma shi ma ya tsira daga zafin wannan cutarwa, don kuwa a dabi'ance mutum yana so ya rayu cikin al'umma wacce take cikakkiya wacce ta tsira daga dukkan cutarwa. To don haka matukar dai al'umma ba su tsira daga cutarwa ba, shi ma ba zai tsira ba, don kuwa shi ma cikin wannan al'umma yake raye. Gaskiya da Wajibi:
Dukkan wata halitta a wannan duniya tamu, tana da wata siffa ta taimakekkeniya da 'yan-'uwanta, tana bayarwa da kuma karba daga 'yar'uwan nata. Misali, mutum, dabbobi, tsirrai da dabi'a, duk suna jujjuya amfani tsakaninsu, da suka hada da iskar "oxygen" da "carbondioxide", abinci, haske, ruwa....da dai sauransu. Haka shi ma mutum, yana rayuwa ne cikin iyali da al'ummarsa, yana alaka da sauran mutane kana kuma suna jujjuya amfanoni a tsakaninsu. Don haka yana da hakkoki a kan iyali da kuma al'ummarsa, kamar yadda su ma suke da hakkoki a kansa.... Ko wane mutum yana da hakki, yana kuma da wajiban da suka hau kansa, to amma wannan daidaituwa ta al'ummance da dokoki na al'umma ba za su taba tabbatuwa ba kana kuma zaman lafiya da kwanciyar hankali ba za su samu ba, har sai an kiyaye wadannan al'amurra.... Hakika duk wanda ya bukaci wani abin da ba hakkinsa ba ne, to ba makawa yana zaluntar sauran mutane ne, don kuwa so yake ya bautar da al'umma. A sabili da haka ne al'umma suke ki da kuma jefar da shi.
|