Hukunce - Hukunce



T26: Shin neman izinin A'alam wajen ci gaba da

takalidin mamaci sharadi ne ko kuma za'a iya neman izinin kowane mujtahidi?

A: Ba wajibi ba ne takalidin A'alam cikin mas'alar ci

gaba da takalidin mamaci, idan dukkan fukaha'u sun yarda da hakan.

T27: Bayan rasuwar Imam (r.a) na zaci cewa ba ya halatta a ci gaba da taklidin mamaci kamar yadda

fatawarsa ta nuna, don haka sai na zabi wani mujtahidi rayayye don in masa taklid to shin ya halatta in sake komawa ga Imam (r.a) a karo na biyu?

A: Ba ya halatta gare ka ka koma gare shi (Allah ya rahamshe shi) bayan ka canza takalidinka cikin dukkan mas'alolin fikihu daga gare shi zuwa ga wani rayayyen mujtahidi, sai dai idan fatawar shi wannan rayayyen mujtahidi ita ce wajibcin ci gaba da takalidin mamacin da yake A'alam kana kuma kai ka yarda da cewa imam (r.a) shi ne A'alam kan wannan rayayyen mujtahidi, to a wannan hali wajibi ne gare ka ka ci gaba da takalidin marigayi Imam (r.a).

T28: Shin wajibi ne ga masu takalidin Imam (r.a) kana kuma suke son ci gaba da yi masa takalid su nemi izinin daya daga cikin rayayyun maraji'ai ko kuwa ittifakin da yawa daga cikin marajiai da many an malamai kan halaccin ci gaba da takalidin mamaci ya wadatar?

A: Ittifakin manyan malaman wannan zamani kan halaccin ci gaba da takalidin mamaci ya wadatar wajen ci gaba da takalidin marigayi Imam (r.a) dan haka babu bukatan sai an koma ga wani takamammen mujtahidi.

T29: Mene ne fatawarka kan ci gaba da takalidin mamaci cikin mas'alolin da mukallafi ya yi aiki da su yayin rayuwarsa da kuma wanda bai yi aiki da su ba ?



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next