Hukunce - Hukunce



saboda la'akari da fatawar  daya daga cikin manyan mujtahidai, to bayan da na yi nazarin amsoshinka cikin "al-lstifta'at" da kuma ra'ayinka kan ci gaba da takalidin Imam khumaini (r.a), sai na bar wancan na ci gaba da ayyukana dai-dai da fatawoyin hnam (r.a) bugu da kari kan fatawoyinka, shin akwai wata matsala a cikin wannan "udul" nawa?

A: Ba ya halatta a bisa Ihtiyat na wajibi canza takalid daga rayayyen mujtahidi zuwa ga wani rayayyen, sai dai idan a ganin mukallafi na biyun ya fi na farkon ilimi kana kuma fatawarsa ta saba wa fatawar na farko, to a wannan halin wajibi ne bisa ihtiyat ya koma ga na biyun.

T23: Wanda ya kasance yana takalidi wa Imam (r.a) kana kuma ya ci gaba da yi masa takalidi (bayan rasuwarsa), shin zai iya komawa ga waninsa na daga cikin maraji'ai cikin wata mas'ala kamar rashin daukar garin Teheran cikin manyan birane ko kuma a'a?

A: Hakan ya halatta a gare shi, ko da yake bai kamata a bar ihtiyat, ba wajen ci gaba da taklidin Imam (r.a), idan har yana ganin fifikonsa kan rayayyu.

CI GABA DA TAKLIDIN MAMACI

T24: Wani mutum bayan rasuwar Imam al-Rahil (r.a) ya yi takalidi wa wani marja'i, to amma a yanzu yana so ya sake komawa ga taklidin Imam (r.a) a karo na biyu, shin hakan ya halatta a gare shi?

A: A bisa ihtiyat canza takalidi daga rayayyen mujtahidi wanda ya cika sharudda zuwa ga mamaci ba ya halatta, na’am idan har shi rayayye bai mallaki sharuddan takalidi ba to komawa gare shi tun farko bai inganta ba, dan haka, kenan har yanzu yana nan a kan taklidin waccan mamacin

kuma yana da zabi imma dai ya ci gaba da taldidin mamacin ko kuma ya koma ga rayayyen mujtahidi wanda ya halatta a yi masa takalidi.

T25: Mene ne hukuncin ci gaba da takalidin mamaci idan har mamacin shi ne A'alam?

A: Bisa dukan hali ci gaba da takalidin mamaci ya halatta ko da yake ba wajibi ba ne, to amma ya kamata kada abar Ihtiyat wajen ci gaba da takalidin mamacin da yake shi ne A'alam.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next