Hukunce - Hukunce



DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

Wannan bayani ne da aka dauko shi daga gabatarwa da kuma babi na farko na Littafin Amsoshi Da Tambaya na Sayyidul Ka’id (H) sai a karanta da fatan ya zama mai amfani ga musulmi gaba daya :

Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya shar'anta halal da haram ya halatta abubuwa masu kyau kana ya haramta munana.Tsira da aminci su tabbata ga manzon tsira Muhammad tare da tsarkakan mutanen gidansa da zababbun sahabbansa. Tun shekaru masu yawa tambayoyi daga kowani yanki na duniya suka dinga isowa zuwa ga ofishin jagoran al'ummar musulmai Ayatullah al-Uzma sayyid Aliyu Khamene'i (Allah Ya kare shi Ya kuma kara masa tsawon rai).

Haka dai wadannan wasiku suka ci gaba da isowa har suka wuce dubu goma, to cikin yaddar Allah Ayatullah Khamena'i ya sami damar amsa wadannan tambayoyi dai-dai da fatawarsa kana wasunsu kuma dai-dai da fatawar mujaddadin wannan karni Ayatullah AI-uzma Al-lmam Ruhullah Al- Musawi al- Khumaini (R.A). To wadannan amsoshi sun kunshi dukkan babobin fikikhu da kuma hukunce hukunce na shari’a- musanman ma wadanda suka zamanto na rayuwan yau da kullun- bugu da ((an kan sababbin mas'aloli na zamani wadanda al'umma suke tsananin bukatarsu. A Saboda haka ne ya sa wadansu daga cikin manyan malamai suka nemi a buga su don muminai su amfana da su. Ko da yake daga farko Ayatullah Khamene'e ya nuna rashin amincewarsa ga hakan, to amma nacewar da Muminai daga ko' ina a duniya suka yi kan a buga

wannan aiki dan su sami abin koyi, wanda hakan ya dada tsanani ne lokacin da wasu manyan malamai ma'abuta sani suka dora al'amarin marja'iyya a kansa da kuma dora masa wannan babban matsayi, ya sanya shi ya yarda da wannan bukata tasu,dan sauke wannan babban nauyi.

To bayan da aka gama tsattsarawa da kuma harhada wadannan tambayoyi da amsoshi an kaddamar da su gare shi domin ya kara dubawa, kuma ya ba da izinin buga shi da yada shi, inda kuma cikin yardar Allah aka samu hakan. Daga karshe muna mika godiyarmu da kuma fatan alheri ga 'yan uwa muminai da suka yi  dawainiyar wannan aiki daga bisani suka kaddamar da wannan ingantaccen aiki domin ya zan mai haskaka tafarki ga muminai, muna rokon Allah ya saka musu da alheri. Bangaren hukunce-hukuncen shari' a Ofishin Ayatullah al-uzma Sayyid Aliyu khamene' i (Allah ya kara masa tsawon rai)

BABIN TAKLID

TAKLID

T1: A, fatawarka, shin aiki da"ihtiyat" shi ya fi ko kuma yin "taqlid"?

A: Kasantuwar aiki da"ihtiyat" ya ta'allaKa ne da sanin wurarensa, kana da kuna sanin yanayin "ihtiyat" din, kuma

ba kowa ya san su ba face mutane kadan, bugu da kari kan cewa aiki da "ihtiyat" yana bukatuwa ga sarrafar da lokaci mai yawa, don haka abin da ya fi shi ne yin taklid ga



1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next