Hukunce - Hukunce



A: Taklidin wanda ba A'alam ba cikin mas'alolin da fatawoyinsa ba su saba wa fatawoyin A'alam ba babu matsala ga hakan.

T12: Dangane da Taklid, wane ne ya wajaba mu yi masa takalidi?

A: wajibi ne yin taklidi ga mujtahidi wanda ya cika sharuddan ba da fatawa da kuma marjaiyya, kana kuma ya kasance A'alam a bisa ihtiyat.

T13: Shin ya halatta a yi taklidi ga mamaci a farkon farawa?

A: Ba a barin ihtiyat a farkon farawa, mutum ya yi taklid ga rayayyen mujtahidi wanda yake A'alam.

T14: Shin takiidin mujtahidi mamaci, ya dogara ne kan taklidin rayayyen mujtahidi ko kuma a'a?

A: Halaccin taklidin mamaci a farkon farawa, ko kuma ci gaba da takalidin mamaci duka ya ta'allaka ne da izinin rayayyen mujtahidi A'alam.

HANYOYIN TABBATAR DA IJTIHADI DA A’ALAMIYYA DA KUMA GANO FATAWA

T15: Shin ya wajaba a gare ni bayan na gano cancantar wani mujtahidi ta hanyar shaidar adilai guda biyu in sake tambayan wasu kan hakan?

A: Yana inganta a takaita ga shaidar adilai guda biyu daga cikin ma'abuta sani (Ahlul khibra) kan cancantar



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next