Hukunce - Hukunce



T44: Hakika ana amfani da kalmar wilayatul mudlaka (iko na gaba daya) a zamanin Manzon Allah(Sawa) da ma'anar cewa shi Annabi(sawa) idan da zai umarci wani mutum da aikata wani al'amari to wajibi ne ya aikata shi ko da kuwa alamarin yana daga lamurra mafi wahala, kamar da annabi (S.A.W) zai umurci wani mutum da ya kashe kansa to wajibi ne ya aikata hakan, to tambaya anan ita ce: Shin "wilayatul mudlaka" har yanzu tana nan da wannan ma'ana ?tare da cewa shi annabi (sawa) ya kasance ma'asumi ne, amma a wannan zamani babu wani jagora ma'asumi?

A: Abin nufi da "wilayatui mudlaka" ga fakih (mujtahidi)

wanda ya cika sharudda shi ne cewa shi addinin musulunci wanda shi ne cikamakin saukakkun addinai wanda kuma zai ci gaba da wanzuwa har zuwa ranar alkiyama addini ne na hukunci da kuma jagorantar al'amurran al'umma, dan haka dole ne alummar musulmai da dukkan bangaronnsu su kasance suna da jagora mai mulkinsu (malami) kuma shugaba wanda zai kare su da addininsu daga abokan gabansu, kana ya kare musu tsarinsu, sannan ya tsayar da adalci a tsakaninsu, ya kuma hana masu karfi su zaiunci masu rauni, ya kuma samar da abubuwan ci gaba na ala’du, siyasa da zamantakewarsu.

Watakila wajen gudanar da wannan al'amari ya yi karo da manufofin wasu ko bukatunsu ko burace-buracensu ko

amfaninsu ko kuma 'yancin wadansu mutane don haka wajibi ne gajagoran musulmai yayin gudanar da al'amarin

jagoranci bisa ga fikihun musulunci da ya dauki matakai da suka dace idan ya ga bukatan hakan.

Kana dole ne ya zamanto ikonsa da kuma abin da ya yi nufin zartarwa ya zama shi ke da rinjaye kan iko da kuma

nufin sauran jama'a a duk lokacin da wadannan manufofi

guda biyu suka yi karo to wannan dan takaitaccen bayani ne dangane da ma’anar

 ALWILAYAL MUTLAKA.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next