Rantsuwa Da Wanin Allah



Dalilan Masu Haramtawa

Masu musun rantsuwa da wanin Allah suna kafa dalilai ne da wasu hadisai guda biyu kamar haka:

1-Manzo (s.a.w) ya ji Umar yana cewa na rantse da babana, Sai Manzo ya ce: LAllai Allah ya hane ku da ku yi rantsuwa da iyayenku, wanda yake so ya yi rantsuwa ya yi rantse da Allah ko ya yi shiru”[14].

 

Amsa

Wannan hadisi ba sheda ba ne ga masu musun wannan al’amari:

Domin kuwa akwai yiwuwar cewa an hana sahabbai da su yi ranstuwa da iyayensu domin iyayensu sun kasance mushrikai ba mutanen kirki ba, don haka irin wadannan mutanen sam ba su da wani matsayi a wurin Allah wanda suka cancanci a yi ranstuwa da su. Abin da yake karfafa wannan magana kuwa shi ne hadisan da zasu zo kasa kamar haka:

“Kada ku yi rantsuwa da mahaifi ko mahaifiyarku ko wani kishiyar Ubangiji”.

“Kada ku yi rantsuwa da iyayenku ko dawagitai”.

Tare da kula da ma’anar wadannan hadisai na sama zamu iya fahimtar abin da wancan hadisi yake magana a kansa, wannan kuwa shi ne Manzo ya hani Umar ne da yin ranstuwa da abin da suke bayyanar da shirka da mushrikai ne, domin kuwa a gefen iyaye ya ambaci kishiyoyin Ubangiji da dawagitai wadanda suke nufin gumaka da abin bauta. Saboda haka manufar Manzo shi ne hani a wani wuri na musamman ne ba dukkan rantsuwar ba.



back 1 2 3 4 5 6 7 next