Rantsuwa Da Wanin Allah



A cikin Kur’ani kusan wurare arba’in ne aka yi rantsuwa kuma Allah yana rantsuwa ne da wasu abubuwa da ba shi ba, misali yakan yi rantsuwa da baure, zaitun, Dotsen Duri sina, Baladil amin, dare da rana, Fajr, Rufi madaukaki, darare guda goma, shafa’i da Wutri, Dur, Kitabul mansur, Baitull ma’amur, Bahrul masjur, da ruhin Manzo:

“Allah yana rantsuwa da itaciyar b‌aure da zaitun, sannan yana rantsuwa da duri sina. kuma yana rantsuwa da garin Makka mai aminci”. [1]

“Allah yana rantsuwa da dare yayin da ya yi duhu, kuma yana rantsuwa da rana yayin da ta haskaka duniya”[2].

“Allah yana rantsuwa da Fajr da darare goma. Sannan yana rantsuwa da shafa’i da wutri. Kuma Allah yana rantsuwa da dare mai duhu yayin da ya koma rana”[3].

“Allah yana rantsuwa da dutsen duri sina, sannan yana rantsuwa da rubutaccen littafi, wanda aka rubuta a cikin takarda mai fadi, kuma Allah yana rantsuwa da baitil Ma’amur, sannan yana rantsuwa da rufi madaukaki, kuma Allah yana rantsuwa da kogi mai igiyoyin ruwa”[4].

“Ina rantsuwa da rayuwarka ya Manzo, lallai sunacikin magagin dimuwa”[5].

Dalilan da suka sanya Allah madaukaki yake rantsuwa da wadannan abubuwa yana iya zama daya daga cikin wadannan abubuwa guda biyu kamar haka:

A- Sanya wa mutum tunanin ya yi bincike a kan sirrinka da suke cikin wadannan abubuwan, ta yadda zai yi tunani a kansu, domin kuwa tunani a kan halitta yana daya daga cikin siffofin masu imani. Sannan Kur’ani yana kira zuwa ga tunani kamar haka:

“Ka ce ku kalla ku gani abin da yake cikin sammai da kassai”[6]. Sannan a wata ayar yana cewa: “Wadanda suke tunani a cikin halittar sammai da kassai, ubangijimmu lallai ba ka halicci wannan ba hakan babu wata manufa, tsarki ya tabbata gareka ka tseratr da mu daga zabar wuta”. [7] Haka nan Allah madaukaki yana rantsuwa da rana da wata, sannan yana rantsuwa da dare da rana, ga abin da yake cewa a cikin Kur’ani:

“Allah yana rantsuwa da rana da haskenta, kuma Allah yana rantsuwa da wata yayin da ya biyo rana, kuma Allah yana rantsuwa da yini yayin da ya yi haske, Kuma Allah yana rantsuwa da dare yayin da ya rufe rana. Sannan yana ranstuwa da sama da abin da ya gina ta. Kuma yana rantsuwa da kasa da abin da ya shimfida ta”.



back 1 2 3 4 5 6 7 next