Rantsuwa Da Wanin Allah



Manufar dukkan wannan rantsuwa shi ne janyo hankalin mutum zuwa ga tunani a kan ayoyin Ubangiji, ta yadda sakamakon haka ya kara karfafa imaninsa da kadaita Ubangiji.

B- Dalili na biyu kuwakan yin wannan rantsuwa shi ne, bayyanar da matsayin wadannan abubuwa na halitta wanda Allah yake yin rantsuwa da su, ta yadda suke da matsayi a wajen Allah madaukaki ta sakamakon haka yake rantsuwa da su, a kan haka ne yake rantsuwa da ran Manzo (s.a.w) inda yake cewa: “Ina rantsuwa da ranka lallai sunacikin magagin dimuwa”.

 

2- Kur’ani Abin Koyi Ne

Kur’ani littafi ne mai shiryaswa kuma abin koyi, yin rantsuwa da wani abu wanda ba Allah ba a cikin Kur’ani yana nuna cewa wannan abin ba shirka ba ne sannan kuma ba haramta ba. Sannan idan irin wannan rantsuwa ya kebanta da Allah ne, ta yadda wasu ba su da hakkin yin irin wannan rantsuwa, to da ya kamata a bayyanar da hakan a cikin Kur’ani ko maganganun Manzo (s.a.w)

Kur’ani yana nuna cewa sifffar “takabbur” (nuna isa) siffar Ubangiji ce, amma hankali da ruwayoyi suna nuna cewa wannan siffa ta girman kai, ta takaita ne kawai ga Allah, wanda yake da dukkan siffofi na kammala da jamala daga zatinsa, ba waninsa ba wanda ba shi da wata kammala sai wacce ya samu daga Allah madaukaki.

Kasantuwar rantsuwa da wanin Allah kusan arba’in a cikin Kur’ani yana bayyanar da cewa idan da wannan aiki ba shi daga kyawawan ayyuka, to ba shi daga cikin ayyuka kuma mararsa kyawu. Kuma idan har irin wannan ranstuwa shirka ce, to yana nufin kenan Allah wanda yake hana mu daga yin shirka, shi da kansa ya aikata hakan! Daga wannan ne zamu fahimci cewa rantsuwa da wanin Allah wanda yake nuna girma da daukakar wanda aka yi ranstuwar da shi, ba shi da wata matsala.

Wadansu wadanda suke fito-na-fito da irin wannan al’amari wanda yake da dalilai masu karfi, sun yi kokarin tawilin wadannan ayoyi ne, ta yadda suka sanya kalmar”Rabb” a farkon irin wadannan rantsuwa, misali suna cewa, idan Allah ya ce ina ranstuwa da rana, wato ma’anarsa ina rantsuwa da ubangijin rana, wato “rabbis shams”, saboda haka idan muka lura rantsuwa guda daya tak kenan ta zo a cikin Kur’ani, wannan kuwa shi ne ranstuwa da Allah! A nan kuwa akwai sauran magana domin kuwa wannan shi ne ake kira da tafsiri da ra’ayi, domin kuwa mai yin wannan tawilin tun farko yana da wata akida sakamakon zahirin wadannan ayoyi ba su dace da wannan akida ta shi ba sai ya fake da yin tawili kamar yadda muke gani!

 

Rantsuwa Da Wanin Allah A Cikin Sunnar Manzo (s.a.w)



back 1 2 3 4 5 6 7 next