Rantsuwa Da Wanin Allah



Rantsuwa Da Wanin Allah

 

Mawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani

Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani

Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id

A fasalin da ya gabata mun yi magana ne a kan hada Allah da wasu bayinsa na gari, wato mutum ya nemi wani abu daga Allah ta hanyar hada shi da matsayin wani daga bayin Allah.

Amma a cikin wannan fasali abin da zamu yi magana a kansa shi ne rantsuwa da wanin Allah. Mu musulmai saudayawa yayin da muke magana da abokanimmu mukan yi rantsuwa da Allah da Manzo da ka’aba da makamantansu, cewa ban yi kaza ba. Ko kuma ina rantsuwa da Kur’ani zan yi kaza, amma ta bangaren shari’a menene hukuncin wannan abu shin ya halasta ko kuwa bai halasta ba?

Kafin mu bayar da amsar wannan tambaya zamu yi bayanin wasu abubuwa guda biyu a matsayin gabatarwa kamar haka:

 

1- Menene Dalilin Rantsuwa Da Wanin Allah A Cikin Kur’ani?



1 2 3 4 5 6 7 next