Rantsuwa Da Wanin Allah



A cikin sunnar Manzo ma akwai misalai da dama dangane da ranstuwa da wanin Allah, don haka a nan zamu kawo wasu daga ciki kamar haka:

1-Muslim yana ruwaitowa a cikin sahih dinsa: Wani mutum ya zo wajen manzon Allah sai ya ce: wace sadaka ce ta fi kowace lada?

Sai Manzo ya ce: “Ka yi ranstuwa da babanka, ya fi ka bayar da sadaka kana mai lafiya alhalin kana tunanin talauci da rashi a kan ci gaba da rayuwarka”[8].

2-Sahih Muslim ya ruwaito a cikin sahih dinsa yana cewa:

“Wani mutum ya zo wajen manzon Allah daga Najad yana tamabaya a kan musulunci? Sai Manzo ya ce masa: Musulunci shi ne salloli guda biyar a cikin dare da rana.

Sai ya ce bayansu akwai wani abu da ya hau kaina? Sai Manzo ya ce masa babu…sai dai ka yi nafila da azumin watan Ramadhan.

Sai ya ce akwai sauran wani abu?

Sai Manzo ya ce babu. Sai dai ka yi nafila. Sai ya ambata masa zakka.

Sai wannan mutum ya ce: “Akwai sauran wani abu? Sai Manzo ya ce babu sai dai ka yi nafila. Sai wannan mutum ya juya yana cewa: wallahi ba ragi ba kari a kan wannan, sai Manzo ya ce masa ka rabauta, ina rantsuwa da babansa idan da gaske yake yi zai rabauta, ko kuma ya ce ina ranstuwa da babansa zai shiga aljanna idan ya zama mai gaskiya a kan a bin da ya fada”[9].

Wannan kuwa ba kawai Manzo ba ne ya yi rantsuwa da wanin Allah, domin kuwa a hudubobin da wasikun Imam Ali (a.s) a wurare da dama ya yi ranstuwa da wanin Allah.



back 1 2 3 4 5 6 7 next