Karamomin Waliyyai



Amma domin ya bayyana cewa babu wani mutum wanda yake iya yin haka ba tare da izinin Allah ba, domin Kur’ani ya nisantar da tunani na shirka ko hada Allah da wani, kuma ya tabbatar da cewa mutum wajen yin halitta yana da bukatuwa zuwa ga Allah, ba wai shi da kansa ba tare da amincewar Allah yake yin ayyukansa ba, Sai ya zamana a cikin dukkan wadannan ayyuka na annabi Isa aka bayyanar da abin cewa duk yana faruwa ne da izinin Allah, wato a cikin kowane abu an kiyaye kadaita Allah a cikin ayyuka wanda yake daya daga cikin matakai na kadaita Allah (s.w.t)

A nan zamu wadatu daga abin da muka yi bayani dangane da mu’ujiza da karamar annabawa da waliyyan Allah a kan cewa duk suna faruwa ne da izinin Allah (s.w.t). Sannan dangane da abubuwan da muka kawo kuwa suna matsayin misali ne daga mu’ujizoji da karamomin Waliyyan Allah wadanda suka zo daga Kur’ani da hadisan Manzo da Nahjul balaga.

Daga karshe zamu yi nuni ne da abin da wasu marubuta suka yi imani da shi cewa yarda da irin wadannan karamomin na waliyyai wani nau’i ne na shirka, amma wannan ya faru ne sakamakon gafalarsu a kan cewa mutum yana iya yin wani abu a cikin duniya ta hanya guda biyu:

1-Ya zamana mutum da kansa ne ya mallaki wannan ikon, wato ya zamana wannan karfin da iko daga gareshi ya samo asali.

2-Karfin da ikonsa ya zamana ya samo asali ne daga Allah madaukaki, Wato sakamakon wasu dalilai yake bai wa wasu daga cikin bayinsa ikon yin hakan.Babu shakka da ma’anar ta farko wani nau’i ne na shiraka da Allah kuma ba ya inganta. Kasantuwar mutum ya zamana yana da iko a kan yin wasu abubuwa wadanda suka sabawa al’ada kuma ya dauka cewa wannan ikon ya same shi daga kansa, to wannan shirka ce kuma hada Allah ne da wani kuma yana kore mutum daga musulunci. Amma fuska biyu kuwa, wannan yana nuna tsantsan kadaita Allah ne, domin kuwa ya samo asali ne daga kudrar Allah wanda yake shi kadai yake.

Idan muka lura kuwa dangane da matsayi da martabobin da Allah ya bai wa wasu daga cikin waliyyansa, bai kamata ba mu yi shakku dangane da abin da muka gani ko muka ji labari na daga karamomi da mu’ujizojinsu suna raye ko kuwa bayan ransu. Domin kuwa karamar Annabi Masih ba ta kebanta ba da rayuwar wannan duniya, domin kuwa ta samo asali ne daga kusanci da yake da shi na ruhi zuwa ga Allah madaukaki, wannan kuwa yananan kiyaye a kowane lokaci, wannan kuwa a wannan duniyar ne ko kuwa a rayuwar duniyar barzahu ce.

Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org

Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)

Facebook: Haidar Center - December, 2012



 



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9