Karamomin Waliyyai



A cikin wannan aya Annabi Isa (a.s) yana jingina wadannan ayyuka zuwa gare shi kamar haka:

1-Halitta tsuntsun daga yumbu.

2-Hura rai ga tsunsu da rayar da shi.

3-Warkar da makahon da aka haifa da makanta.

4-Warkar da kuturta.

5-Rayar da matattu.

Annanbi Isa duk yana jingina wadannan ayuka zuwa gare shi, ba wai yana rikon ba ne daga Allah da gudanar da hakan. Domin kuwa yana cewa: “Ina yin wadannan abubuwa ne da izinin Allah”amma a nan menene hakikanin izinin Ubangiji? Shin wannan izini ta hanyar lafazi ne? Tabbas ba haka ba ne, wannan izini na boye ne. Wato ta yadda Allah madaukaki yake bai wa bawansa wannan karfi ta yadda zai iya gabatar da wadannan ayyuka.

Sheda kuwa a kan ingancin wanann tafsiri shi ne, bawa ba wai kawai a cikin abubuwa da suka saba wa al’ada yake mabukaci ba, har a cikin abubuwan da suke na al’ada mabukaci ne, domin kuwa babu wani aiki da zai yiwu ba tare da izinin Allah ba, iznin Allah kuwa a cikin komai shi ne, ya bai wa mutum karfi da rahamar da zai iya gabatar da wannan aikin. Don haka ne a cikin wannan aya da muka ambata annabi Isa yake jingina wadannan ayyuka zuwa gare shi. Sannan a wata ayar ma Allah da kansa a fili yake jingina wadannan ayyuka zuwa ga annabi Masih (a.s) wannan kuwa yana tabbatar da wannan al’amari kamar haka:

“Kuma yayin da kake halitta daga yumbu kamar siffar tsuntsu da izinina, sannan ka hura masa rai sai ya zama tsuntsu duk da izinina, sannan kana warkar da makaho da mai ciwon kuturta da izinina, sannan ka rayar da matattu da izinina”[16].

A cikin wadannan ayoyi dole mu kula da kyau, wane ne mai aiwatar da wannan aiki, domin kuwa ba yana cewa: Ni ne na halicci wannan kaza ba, ko ni ne na warkar da wannan makaho, ko ni ne na tayar da wannan matacce. Yana cewa ne: “Yayin da kake halitta, ko “Kake warkar” Ko “Yayin da kake rayar da”. Wane bayani ne ya fi wannan bayyana?



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 next