Karamomin Waliyyai



Rashin kula da jin dadi na jiki yana sanya wa mutum ya samu wani karfi na musamman da bangaren ruhinsa. Wato kai ka ce akwai kishiyanta tsakanin jiki da ruhi. Domin kuwa duk lokacin da mutum ya bai wa jikinsa kula ta musamman ta yadda ya nutse a cikin jin dadi da sha’awar abin duniya, wannan kulawa da nutsewa cikin tarbiyar jiki yakan sanya mutum ya gafala da bangaren ruhinsa, ta yadda ba zai kula da abin da ya shafi tarbiyar ruhin ba. Haka nan duk lokacin da mutum ya kawar da kansa daga sha’awar abin duniya da jin dadi, sannan ya kula da abin da ya shafi a bangaren ruhinsa, sakamakon haka zai iya samun wani karfi da iko da bangaren ruhinsa, ta yadda zai kara karfin bisa ga wanda yake da shi na al’ada.

Masu tarbiyyar ruhi mai nauyi wacce ma ta saba wa ka’idojin addinin musulunci kuma musulunci yake ganinta a matsayin haram, sun kawar da kansu daga duk wani nau’i na kula da jiki. Wannan nau’in tarbiyya kasantuwarta mai tsananin wahala da azabtarwa ya sanya ba kowane mutum ne ba yake iya jure ma ta. Har suma wadanda suka bi wannan hanya ba kai tsaye suke shiga a ciki ba, sukan bi a hankali ne har su saba, ta yadda sakamakon bi daki-daki a hankali suna kara matsawa gaba.

Babbar manufarsu a kan wannan aiki kuwa shi ne ta yadda mutum zai samu damar da zai iya kaucewa duk wani soyace-soyacen abin duniya da tasirinsa a kansa, sakamakon rashin kula da abin duniya, zai samu karfin ruhi. Babu shakka wannan nau’i na tarbiyya ya sabawa halittar dan Adam da shari’ar musulunci. Domin kuwa wani nau’i ne na isar da cuta ga jiki da rayuwar dan Adam. Sannan kuma wani nau’i na koyi da abin kiristoci suke yi a kaurace wa dukkan rayuwa wacce shari’ar musulunci ta yi hani a kansa.

2-Ta Hanyar Ibada

Hanya ta biyu kuwa kuma ingantatta da ake bi domin samun wannan karfi da iko na musamman ta hanyar ruhi, ita ce bin hanya mikakka ta bin Allah da bautarsa. Ta yadda mutum zai sanya hukunce-hukuncen addinin musulunci shi ne ma’auni a wurinsa, wato mutum ya tarbiyyantar da ruhinsa ta hanyar bin abin da Allah madaukaki ya umurci bayinsa da su aikata. Domin ayyukan ibada na zahiri ba shi ne ba Allah yake bukata, idan har musulunci ya yi umarni da aikata su ba don komai ba sai domin fa’idar da suke da shi ga mutum. Wato saboda kusancin da take sanya wa tsakanin mutum da Ubangiji da kuma kamalar da yake samu ta hanyar hakan. Masu imani da farkon lokacin da suke aiwatar da ayyukansu na ibada, ba tare da zabinsu ba sun fara hawa hanyar samun kammala, sannan suna tanajin wani karfi na musamman ne ta hanyar ruhinsu. Babu shakka ta wannan hanyar kamar da mutane zasu samu ta bambanta da ta juna, haka nan matsayin da kowane zai samu ya bambanta da na wani, wannan kuwa yana faruwa ne domin yawan biyayya ga Allah da bautar da kowane mutum yake yi ba iri guda ba ne.

Manzo (s.a.w) a wani hadisi ya bayyana matsayi da martabar da wadanda suka hau hanyar Allah suke da shi, ga kuma abin da ya ruwaito daga Allah madaukaki: kamar haka: “Babu wani aiki da bawa zai kusance ni da shi kuma na fi soyuwa gare shi kamar ayyukan da na wajabta ga bawa, kuma bawa bai gushe yana kusantata da nafiloli ba sai na so shi, idan kuwa na so shi zan zama jinsa wanda yake ji da shi, in zama ganinsa wanda yake gani da shi, sannan in zama hannunsa wanda yake kai hari da shi, kuma in zama kafafunsa da yake tafiya da su, idan ya roke ni tabbas zan ba shi abin da yake bukata, idan kuma ya nemi tsarina zan rsare shi”[1].

Tare da kula da abin da wannan hadisi yake koyar da mu zamu gane irin matsayin da zamu iya samu sakamakon yin bautar da aka wajabta mana da sauran nafiloli, sannan kuma ta wannan hanyar ne mutum za samu wani karfi a musamman ta yadda zai iya jin wani sauti daga Allah wanda ba kowane yake iya jinsa ba, sannan zai rika ganin wasu abubuwa wadanda ba iya ganinsu da idanuwan da kowa yake da su. Sannan kuma sakamakon wadannan ayyuka da matsayi da ya samu a wajen Allah duk abin da yake za a biya masa bukatarsa. A cikin kalama guda daya zai zama masoyin Allah, sannan ayyukansa zasu zama ayyukan Allah.

Babu shakka abin da ake nufi da cewa Allah zai zama ji da ganin mutum shi ne, zai kasance idanuwansa sakamakon kudura da ikon Allah suna ganin da ba kowane yake yin irinsa ba, haka nan kunnuwansa suna ji fiye da na sauaran al’umma, sannan zai samu karfi mai yawa.

Manzo (s.a.w) dangane da cancantar dan Adam ya isa ya zama abin mamaki inda yake cewa, hanyar ibada ita ce hanya kawai ingantacciya kuma marar hadari da mutum zai iya bi domin ya samu gani da ji na musamman da sauran martabobi a wajen Allah (s.w.t).

A yanzu zamu yi nuni ne da wasu abubuwan mamaki dangane da sakamakon bin hanyar bautar Allah da bin hanyar Allah wacce take mikakka babu karkace. Ta hanyar kafa hujja musamman da ayoyin Kur’ani zamu tabbatar da yadda mutum zai iya samu iko a kan zuciyarsa da ruhinsa, har ma ya iya samun iko a kan duniyar halitta. Sakamakon biyayyarsa ga Allah (s.w.t), amma dukkan wannan yana samunsa ta hanyar izinin Ubangiji. Wadannan abubuwa kuwa da zamu yi nuni da su, su ne kamar haka:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 next