Karamomin Waliyyai



 

1-Fin Karfin Zuciya

Abu na farko da mutum zai samu sakamakon ibadarsa zuwa ga Allah shi ne, fin karfin zuciyarsa a kan wasu abubuwa da suke aibu ne gare ta. Sakamakon haka ne “Nafsul insani” zata samu daukaka a kan “nafsul ammara” wacce take umurtar mutum da aikata abin da zai tauye shi daga zuwa samun kammala. Mutum ta hanyar ibada da kamalar da yake samu zai kai wani wuri da zai samu karfi a kan wannan “nafsul ammara” ta yadda wannan mutumin yake iya fin karfin abin da zuciyarsa take so na barna. Idan mutum ya kai wannan matsayi na kammala ana cewa ya samu wilaya a kan nafs dinsa, ga abin da wadannan ayoyi suke fada dangane da hakan:

1-“Lallai salla tana hani daga alfasha da abin ki”[2]. Wato mutum sakamakon sallar da yake yi zata samar masa da wani yanayi wanda zai hana shi yin sabo da zunubi.

 

2-Gani Na Musamman

Yana daga cikin fa’idar ibada zata sanya mutum ya zama yana ganin wasu abubuwa na musamman ta yadda yana iya gane gaskiya da bata, saboda haka ba zai taba bace hanya ba. “Yaku wadanda kuka yi imani idan kuka ji tsoron Allah zai sanya muku rarrabewa”, wato zai ba su wata baiwa wacce zasu iya gane gaskiya da karya[3].

Sannan a wata aya yana cewa: “Wadanda suka yi kokari a cikin bimmu zamu shiryar da su hanyoyinmu”[4]

A cikin aya ta uku kuwa yana cewa: “Ya ku wadanda kuka yi imani ku ji tsoron Allah ku yi imani da manzonsa, zai ba ku nau’i biyu na daga rahamarsa, sannan ya sanya muku haske wanda zaku rika tafiya tare da shi”[5].

Abin da kuwa wannan ayar take karantarwa shi ne sakamakon imani da tsoron Allah suna sanyawa su rika jagorantar mutum a duk tsawon rayuwarsa a wannan duniya a kan hanyar da ta dace.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 next