Karamomin Waliyyai



Na uku: Mutum Na biyu kuwa cewa ya yi: Ni zan zo maka da shi kafin ka bude idonka, kuma wannan aiki da ya sabawa al’ada ya jingina shi zuwa ga kansa; “Zan zo maka da shi”.

Idan a nan Kur’ani yana so ya bayyanar da hakikanin wannan al’amari cewa: Ruhin waliyyan Allah da na sauran manyan bayin Allah yana da tasiri wajen aiwatar da mu’ujiza ko karama, ta wace hanya ce zai bayyanar da haka wanda ya fi wannna bayyana, ta yadda masu shakku na wannan zamani kada su yi tawili ko suki yarda da hakan.

Na hudu: Karfin ikon mutum na biyu kuwa wannan aiki babban abin mamaki ne domin kuwa Allah yana bayyanar da cewa sakamakon iliminsa ne da littafi. Ilimin da ya fita daga ikon sauran mutane, wannan ilimi ya kebanci wasu daga cikin manyan bayin Allah. Sannan ana samun irin wannan ilimi ta hanyar kusanci wasu bayin Allah da shi ubangijin, a kan haka ne yake cewa: “Sai wanda yake da ilimi daga littafi ya ce”.

 

C- Ubangiji Dangane Da Annabi Sulaiman A Fili Yana Cewa:

“Duk ta bangaren da yake so haka iskan yake kadawa. Duk da cewa iska yana karkashin tsarin halitta ne amma yakan canza hanya kamar yadda annabi Sulaiman yake so: “Sulaiman yana da iska mai kadawa, wacce take tafiya da umurninsa zuwa kasar da muka yi albarka gareta, kuma mun kasance muna da masaniya a kan komai”[14]. Abin lura a nan shi ne, a fili ayoyin da muka ambata a sama suna bayyanar da cewa wannan iska yana tafiya ne da umurnin Sulaiman.

A wata aya kuwa ana bayyanar da cewa wannan iska wanda Sulaiman yake amfani da shi a matsayin na’urata yadda daga safiya zuwa Zuhr yana tafiyar da sai an dauki tsawon wata guda za a yi ta, sannan daga Zuhr zuwa dare zai iya yin wata tafiyar wata guda ta hanyar sika, wanda a wannan lokacin abubuwan da ake amfani da su wajen tafiye-tafiye, sai an yi wata biyu ana tafiya sannan a yi tafiyar da zai yi a cikin yini guda daya tal.

Lallai Allah ne ya hore masa wannan iska wanda yake iya yin wadannan tafiye-tafiye da shi ya kuma sarrafa shi yadda yake so. Amma jumlar da take cewa: “yana tafiya da umurninsa” wannan a fili yana bayyana cewa Sulaiman yana da tasiri wajen tafiyar da wannan halitta da yin amfani da ita ta yadda ya so, ta yadda yake tafiyar da iska zuwa wajen da ya so, sannan ya tsayar da shi idan ya so hakan.

D-Mu’ujizar Annabin Allah Isa (a.s)

Kur’ani mai girma ya jingina wasu ayyukan da suka sabawa al’ada zuwa annabi Isa (a.s) dukkan wadannan ayyuka suna faruwa daga karfinsa na badini ta hanyar ruhinsa, kamar yadda yake cewa: “Lallai ina halitta muku wani abu mai kama da tsuntsu daga yumbu, sai in hura a cikinsa, sai ya zama tsuntsu da izinin Allah, Sannan ina warkar da mai kuturta da makaho wanda aka haifa da makanta, kuma in rayar da matattu duk da izinin Allah”.[15]



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 next