Rayuwa Bayan Mutuwa



A-Jikin mutum wanda yake a fili, wanda sakamakon dadewa a cikin kasa zai lalace ya yi dai-dai a cikin kasa.

B-Hakikanin dan Adam wanda ake nuni da shi a cikin wannan aya kuma wanda mala’ika zai dauka, yana wurin Ubangiji kuma ba zai taba lalacewa a cikin kasa ba.

A hakikanin gaskiya wannan aya tana ba da amasa ne dangane da wata hujja ta ilimin kimiyya, wannan kuwa ita ce: Wannan abin wanda yake lalacewa a cikin kasa, ba wani ba ne illa abi ya rufe hakikanin mutum, amma abin da yake shi ne hakikanin dan Adam yana hannun mala’ikan mutuwa, sannan kuma za kasance a wurin Allah ba tare da ya lalace ba. Wannan kuwa yana tabbatar mana da cewa hakikanin dan Adam ba wannan jikin ba ne wanda yake lalacewa a cikin kasa, hakikaninsa wani abu ne daban wanda yasha bamban da jiki, sannan duk wasu siffofin jikin ya nisanta daga gare su, (Saboda haka kamar abin da ya shafi rubewa ko lalacewa da bata a cikin kasa duk ya koru a gare shi).

Saboda haka ayoyin da muka ambata a baya da abubuwan da suka zo a cikin ilimin kimiyya duk suna tabbatar da cewa hakikanin dan Adam ba wannan jikin ba ne wanda zai iya lalacewa a cikin kasa. Hakikanin dan Adam wani abu daban ne wanda yake saman wannan jiki, wanda kuma ba ya canzawa, kowane lokaci yananan a tabbace ba tare da wani canji ba.

Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org – www.haidarcip.org

Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)

Facebook: Haidar Center - December, 2012



[1] -A duba asalatur ruh az nazari kur’an.

[2] Isahrat bu Ali Sina:2:292-293 Shifa bangaren dabi’iyyat:282.

[3] -Dairatul ma’arif farid wujdi a karkashin kalmar wahayi da ruhi.

[4] -R. k littafin rayuwa bayan mutuwa wanda lu’un Dani ya rubuta:78-82. wannan an hakaito shi domn karfafa cewa akwai ruhi ne, ba hukuncinsu ko karfaf cewa akwaialaka da ruhi ba.

[5] -Zumar :32.



back 1 2 3 4 5 6 7