Rayuwa Bayan Mutuwa



Da wata ma’ana matakan rayuwar mutum suna farawa ne daga yarinta, bayan wani lokaci zai wuce zuwa samartaka har zuwa tsufa, ta yadda duk zai tamuke, amma akwai wata hakika wacce duk tsawon wannan zamani da matakai tananan a tabbace kuma dukkan wadannan abubuwa suna bi takansa ne. Ta yadda mutum zai ce “wata rana na kasance yaro, wani lokaci kuma matshi, yanzu kuma na manyanta na tsufa”. Duk da cewa mutum ya samu cikakken canji a jikinsa, amma akwai wata fuska inda bai canza ba, ta yadda yana jin cewa duk wadannan matakai sun bi takan wannan hakika ne. Idan da hakikanin mutum ya kasance wannan jikin nasa ne, ba zai taba samun wannan tabbatuwa ba da ya samu ta wata hanya, (Inda yake jin cewa shi ne lokacin da yake yaro yanzu ma shi ne bayan ya tsufa) domin kuwa dukkan jikinsa ya canza saudayawa, ta yadda a bisa wannan hanya ta rayuwa ya kasance da jiki daban-daban. Saboda haka hakinin mutum ba zai yiwu ya takaita ba a jikinsa wanda yake duk bayan lokaci yana canzawa, tabbas a bayan wannan jikin mai canzawa akwai wani abu wanda shi ba jiki ba ne, ta yadda kodayaushe yana nan ba tare da canji ba kamar yadda jiki yake samun canji, sannan ya zamana yana karbar canjin da jiki yake samu a kodayaushe. Sannan ya ci gaba da tafiyarsa har ya kai inda yake so ya kai.

Idan muna so mu yi bayanin wannan al’amari wanda ake iya gwada shi domin tabbatarwa yana iya kasancewa kamar haka:

1-Mutum yana jin wani abu tare da shi wanda kowane lokaci ba ya canzawa wannan kuwa shi ne “ni”

2-Dukkan kwayoyin halittar jikin mutum bayan shekara takwas suna canzawa baki dayansu.

Saboda haka wannan kalma ta “ni” ba jiki ba ce, wani abu ne daban ba jiki ba, domin kuwa idan da hakikanin mutum jiki ne, babu yadda mutum zai rika jin wannan hakika tsayyya wacce yake jingina al’amuransa gareta. Sannan ba zai yiwu ba kotu ta hukunta mutumi dan shekara 40 ba, wanda ya aikata laifi tun yana dan shekara 20, domin kuwa wannan jikin ba shi ne yanzu ba, saboda ya canza dukkan shi, yanzu wani mutumne na daban!

3-Rashin mantawar mutum da kansa yayin da yake mantawa daga dukkan jikinsa. Mu dauka cewa mutum yana cikin wani lambu wanda yake da yanayi mai dadi ta yadda babu sanyi ko zafi mai matsawa, ko kuma iska wanda zai janyo karar ganyen itatuwa, ko tsuntsaye masu kuka ta yadda zasu ja masa hankali, Sannan babu karar komai wanda zai iya zuwa ga kunnuwansa. Wato akwai cikakkiyar natsuwa a wannan wuri ta yadda babu wata matsala ko wani abin damuwa, a wannan lokaci mutum ya yi kokari ta yadda zai yanke tunaninsa ga komai sai kansa, a hankali har ya manta da dukkan gabobinsa, a wannan lokaci zai kasance cikin wata irin mantuwa ta gaba daya, amma akwai wani abu guda wanda bai manta da shi ba, wannan kuwa ba wani abu ba ne hakikanin kansa, sam ba zai manta da kansa ba, duk da cewa ya manta da dukkan gabobinsa, wannan hakika ita ce wacce mutum duk cikin halin da ya shiga ba zai manta da ita ba, saboda haka wannan abu wani abu ne daban wanda ba jiki ba, domin kuwa duk abin da yake daga jikinsa yana cikin kogin mantuwa.[2]

A cikin bayanin wannan hujja babu bukatar doguwar gabatarwa, wato ana iya yin bayaninta a takaice, wannan kuwa shi ne kamar haka cewa, wani lokaci mutum yakan shiga cikin zurfin tunani ta yadda zai manta da komai koda kuwa wani muhimmin abu zai faru a kusa da shi ba zai kula da abin da yake faruwa ba, amma a wannan lokaci ba zai manta da wani abu guda ba, wannan kuwa shi ne kansa. Wato shi mutum ne da yake cikin halin tunani, wannan kuwa shi ne yake bayyanar da hakikanin dan Adam, abin da yake bayan jikinsa da gabobi, wadanda suka kasance ya gafala da su a cikin halin da ya shiga na tunani kamar yadda muka yi bayani a baya.

 

4-Hakikanin ruhi a ilimin kimiyya

Zuwa yanzu mun fahimci wata hakika wacce ita ba jiki ba ce mai suna ruhi. Abubuwan da muka ambata a baya kuwa duk sun kasance cikin abubuwa wadanda za a iya gwadawa domin tabbatar da cewa lallai ruhi wani abu ne wanda ba jiki ba (mujarrad) Sannan mafi yawan mutane suna iya fahimtar wannan sannan ya haifar musu da yakini a kan wannan magana.



back 1 2 3 4 5 6 7 next