Rayuwa Bayan Mutuwa



Amma yanzu domin mu kammala wannan bahasi bari mu koma ga wata kungiya wacce aka kafa ta ilimi a karni na sha tara wacce ta fara da sanin hakikanin dan Adam, ta yadda idan ra’ayin falsafa da ilimin gwaje-gwaje (Science) sun bayyanar da wannan al’amari sannan sai mu koma zuwa ga al’Kur’ani da Sunna domin mu ga hukuncin da zasu yi a kan al’amarin.

A shekara ta 1882 an kafa wata kungiya mai suna “kungiyar bincike a kan ruhi’wacce Babban masanin nan kuma malamin jami’ar Kambirij (Cambridge) mai suna Jomik yake jagoranta wannan malami ya kasance daya daga cikin masanan kasar Birtaniya.

“Yan wannan kungiya kuwa sun hada da mutumin nan da ake yi wa lakabi da suna Darwin, Wiliam wanda yake babban malamin kimiyya ne na kasar Engila, Fedrik, Hursen wadanda suke malaman Jami’a ne a Kasar Amurika Da sauran manyan masanan kimiyya shararru na duniya…

Wannan gungu na masana suka ci gaba da bincike a kan al’amarin ruhi, suka kuma rubuta littafai a kan hakan, ta yadda a cikin shekaru 45 zuwa 50 suka rubuta littafai kusan hamsin a kan wannan magana da muka ambata a sama. Ta yadda sakamakon taimakonsu ne aka warware matsaloli da yawa a kan abin da ya shafi haka.

A hakikanin gaskiya Allah madaukaki ya bude wasu hanyoyi na ilimi a wannan zamani ta yadda dan Adam zai iya fahimtar cewa mutum yana da wani bangare wanda ba jiki ba ne kuma wajen ci gaba da rayuwarsa yana iya amfani da wannan shi kadai don ya ci gaba da rayuwa.[3]

Ilimin da ya shafi alaka da ruhi wanda a wannan zamani wato karni na sha tara aka kirkire shi, ya yaye hijabi zuwa wata duniya wacce ba wannan ba, ta yadda ya bai wa mutum dama ta yadda zai iya alaka da waccan duniya.

Ta bangaren abubuwan da aka tabbatar daga duniyar ruhi ta hanyar kirawo ruhi, yana iya ba da sakamako a kan cewa, lallai bayan wannan duniya ta jiki akwai wata duniyar wacce ba ta jiki ba. Sannan kuma tabbas ba zai gushe ba sakamakon mutuwa, don haka alakar da take akwai tsakanin ruhunan mutanen da suka mutu da mutanen da suke rayuwa a wannan duniya yana tabbatar da cewa lallai ruhuna sunanan bayan mutuwa.[4]

Wannan bahasi kuwa har zuwa yanzu yana ci gaba a yammacin duniya, saboda haka wanda yake ganin kimar abin da ya zo daga kasashen turai yana iya amfani da wannan domin ya kara samun tabbas a kan samuwar wata duniya wacce ba wannan ba.

Da wannan ne bayan mun yi bayani a kan ra’ayoyin masana kimiyya dangane da wannan magana a yanzu zamu koma zuwa ga Kur’ani domin muga hukuncinsa a kan hakan, sannan muga yadda Kur’ani yake bayyana hakikanin dan Adam.

Kur’ani Yana Tabbatar Da Ruhi Ba Jiki Ba Ne



back 1 2 3 4 5 6 7 next