Rayuwa Bayan Mutuwa



Haka nan batun abin da ya shafi kaddara duk da cewa Bahasi ne na falsafa amma kuma ya shafi kowane mutum wato kowa yana so ya san menene hakikanin wannan al’amari. Duk da cewa ba tunanin kowa bane yake iya gane hakikanin al’amura, amma masana falsafa wadanda suke zurfafa tunaninsu suna iya gano hakikanin al’amura ta hanyar tunaninsu.

Sanin abin da zai faru bayan mutuwa ya kunshi wasu batutuwa guda uku da suka shafi mutum kamar haka:

1-Shin menene hakikanin dan Adam, wannan jikin nasa shi kawai ne babu wani abu bayan wannan, ko kuwa hakikanin mutum wani abu ne daban ba jikinsa ba sai dai yana da alaka da jikinsa.

2-Menene hakikanin mutuwa, shin mutuwa shi ne karshen rayuwa ko kuwa wata kofa ce ta shiga wata sabuwar rayuwa a wata duniya?

3-Idan mutum ya mutu ba shi ne karshen rayuwarsa ba, mecece alakar da take akwai tsakanin wannan rayuwar da waccan rayuwar?

A nan zamu yi magana ne dangane da wadannan muhimman batutuwa guda uku:

 

Asali Na Farko

Menene hakikanin dan Adam?

Shin hakikanin dan Adam ya takaita ne kawai ga jikinsa, ko kuwa wannan jikin ya rufe wani abu ne wanda shi ne hakikanin mutum? Da wani kalamin shin wai hakikanin mutum wannan jikin ne kawai babu wani abu wanda ake kira “ruhi”? Ko kuwa bayan wannan jikin akwai wani abu wanda shi ne hakikanin dan Adam, wannan jikin kawai yana matsayin na’ura da yake amfani da ita ne?



back 1 2 3 4 5 6 7 next