Rayuwa Bayan Mutuwa



Ayoyi da dama a cikin Kur’ani suna bayar da shedar cewa ruhi ba jiki ba ne kuma ba shi da duk wasu alamomi na jiki, ta yadda yake nuna cewa hakikanin mutum bai takaita ba ga wannan jiki. Ba ma kawai haka ba, domin kuwa wannan jiki bai wuce wata na’ura ba wacce mutum yake amfani da ita, saboda haka hakikanin mutum shi ne ruhinsa. Ayoyin da suke magana kuwa a kan hakan suna da yawa, amma a nan zamu kawo wasu ne daga ciki a matsayin misali:

1-Daukar rayuka yayin mutuwa:

A nan Allah madaukaki yana tunatar da mutum cewa yana daukar rayukan dan Adam yayin mutuwa da barci, saboda haka wanda yake lokacin mutuwarsa bai riga ya zo ba, sai a mai do masa ransacikin jiki. Kamar yadda yake cewa:

“Allah yana daukar rayuka yayin mutuwa da lokacin barci, wadanda mutuwarsu ta zama tabbas sai a rike ruhinsu, amma wasu rayukan a kan rike su ne zuwa wani lokaci (masu barci), a cikin yin hakan akwai aya ga masu tunani”[5]

Kalmar “Tawaffa” wacce ta zo a cikin wannan aya tana nufin kama abu ne baki dayansa ba tana nufin kashewa ba. Saboda haka zuwan wannan kalama yana nuna cewa a lokacin mutuwa da barci akwai wani abu wanda ba jiki ba wanda Allah madaukaki yakan dauke shi. A wannan lokaci rayukan wadanda mutuwa ta zama tabbas a kansu sai ya rike ruhinsu, Sannan kuma yakan saki rayukan wadanda mutuwa ba ta kai ga zama tabbas ba a kansu, wato lokacin mutuwarsu bai riga ya iso ba, sai ya mai da musu rayukansu, ta yadda zasu ci gaba da shugabancin jikunnansu da shi. Saboda haka idan har da jikin mutum shi ne hakikarsa to amfani da kalmar “Akz, irsal da Imsak” wadanda suke da ma’anonin dauka, aukawa da rikewa, zasu zama ba su da ma’ana a nan. Domin kuwa suna iya zama sun dace da ruhi amma ba su dace ba da jiki a nan, domin kuwa yayin da mutum yake barci ko ya mutu muna iya ganin ransa bai tafi ko’ina ba.

2-Hakikanimmu yana wurin Allah

Kur’ani mai girma ya dauka daga abin da mushirikai suke cewa yayin da suke inkarin tashin kiyama yana cewa:

“Yanzu bayan jikin ya lalace a cikin kasa sannan a ce za a sake tayar da mu”? Wato a cikin wannan aya suna cewa yayin da mutum ya mutu kuma jikinsa ya lalace ya koma kasa, to sam ba zai yiwu ba a sake harhada shi sannan a tayar da shi.

Jawabin da Kur’ani yake baiwa mushrikai kuwa a kan wannan magana tasu yana karfafa abin da muka fada, inda yake cewa, hakikaninsu ai a wajenmu take, wato wannan abin yake lalacewa ya kuma koma kasar ba shi ne hakikaninsu ba. Ga abin da Kur’ani yake cewa: “Ka gaya musu ana horon mala’ikan mutuwa da kama rayukanku, wanda kuma aka wakilta shi akanku, a wannan lokaci zaku koma zuwa ga ubangijinku”.

Kamar yadda muka ambata a ayar da ta gabata cewa kalmar “Tawaffa” ba tana nufin kashewa ba ne, wannan kalma tana nufin dauka kokamawa ne, saboda haka wannan yana nuna cewa mutum bayan mutuwa yan kasuwa ne zuwa gida biyu:



back 1 2 3 4 5 6 7 next