Ziyarar Kaburbura Masu Daraja



 Idan da ziyartar kabarin ‘yan uwa ya kasan ce wani aiki ne daya haramta, mai makon Manzo ya umurce da yin hakuri zai ce ma ta ne ke wannan aiki naki ya haramata a fili, amma sai ya umurce ta da yin hakuri a kan abin da ya same ta ba wai ta nisanci kabarin ba.

 

Amsar wasu tambayoyi guda biyu

 Wasu sun haramta ziyarar mata zuwa kaburbura, suna kafa hujjarsu ne kuwa da wadannan hadisai guda biyu kamar haka:

1-”Allah ya la’anci mata masu ziyarar kabari”

Amsa:

 Wannan Hadisi ya rasa sharuddan da ya kamata ya kasance yana da su kafin a iya kafa hujja da shi. Domin bisa ga dogara da dalilai da aka ambata a baya dole ne mu dauka wannan hadisi an shafe shi, Sannan cikin sa’a wasu daga cikin malaman hadisi na Sunna sun dauki wannan hadisi matsayin shafaffe. Tirmiz maruwaicin wannan hadisi yana cewa: Wannan hadisi an shafe shi lokacin da kafin halasta ziyartar kabari ne, amma lokacin da Manzo ya halasta ziyarar kaburbura wannan hukunci ya hade mace da namiji babu bambanci.

 Kurdabi yana cewa: Wannan hadisi yana Magana ne a kan matan da suke bayar da dukkan lokacinsu a makabarta ne, ta yadda sakamakon haka ba su bayar da hakkokin mazansu da ya hau kansu. Kuma sheda a kan haka shi ne Manzo ya yi amfani da kalmar “Zuwwar” wadda take da ma’anar kambamawa, wato wadanda suke yi yawaita ziyara.

2-Ibn maja yana ruwaito daga Ali Bn Abi Dalib cewa: Manzo (s.a.w). Ya fito sai ya ga wasu mata a zaune, sai ya tambaue su me ya sa suke zaune? sai suka ce: Muna jiran jana’iza ne.

Sai ya ce zaku yi wa jana’izar wanka ne?



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 next