Ziyarar Kaburbura Masu Daraja



 A nan dole mu yi tunatar wa akan wani al’amari shi ne, addinin musulunci addini ne wanda ya dace da halitta mutum, kuma mai sauki, Manzo yana cewa: “Akidun musulunci akidu ne tabbatattu duk wanda zai shiga cikinsu ya shiga tare da dalilai na hankali”.

 Mu dauka cewa mahaifiyar mumini sai ta rasa danta aka kuma rufe shi a karkashin kasa, sai ta damu a kan hakan, abin da kawai zata iya yi a nan shi ne ta ziyarci kabarinsa. A nan idan aka hana ta yin wannan aiki wanda ya dace da hankali kuma dukkan mutanen duniya sun tafi a kan hakan, wannan zai haifar da muguwar damuwa ga zuciyar uwa. Shin musulunci zai yi hani da irin wannan aiki sannan kuma ya zama addini mai sauki?

 Kai asali ma ziyarar kaburbura wani darasi ne kuma mai sanya mutum ya rika tunawa da lahira wanda kuma ya kunshi karantawa wadanda aka ziyarta fatiha. Ta yaya za a hana mata dangane da samun wannan falala?

 Da wani kalamin kasantuwar hikimar ziyarar kaburbura tana kunshe da daukar darasi da tunawa da lahira, ta yaya za a kebance maza kawai ban da mata a ciki?

 Kasantuwar ziyarar kaburbura ya nisanta da duk wani sabo, idan muka dauka haka kuma sai aka hana mata a wancan lokaci, to kila sakamakon cewa ba su kiyaye sharuddan da suka kamata ne.

Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org – www.haidarcip.org

Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)

Facebook: Haidar Center - December, 2012

 



[1] Sunanu Ibn Maja: 1: 500hadisi na 1569.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 next