Ziyarar Kaburbura Masu Daraja



 Da wani kalamin muna iya cewa ziyarar kabarin wani nau’i ne na girmama su. Sakamakon an kashe shahidi a kan wani abu mai tsarki da yake girmamawa, duk wanda ya ziyarci shahidi ya girmama shi, a hakikanin gaskiya ya girmama wannan akidar ne wadda a kanta ne aka kashe shi, sannan yana daukar kansa wanda yake biyayya akan wannan hanya.

Ziyarar Kabarin Manzo (s.a.w)

 Ziyarar Kabrin Manzo mai girma (S. A.W) ko kuma Magjinsa mai tsarki (a.s) bayan girmama su a kan abin da suka yi na sadaukar da rayukan su wajen shiryar da al’umma zuwa ga hanyar Allah, Shi ma yana da hukuncin yi musu bai’a. Imam na takwas (a.s) a cikin maganganunsa dangane da ziyarar kaburburan ma’asumai (a.s) yana cewa: Kowane Imami yan da alkawari tsakaninsa da mabiyansa ziyar kabarin Imamai daya daga cikin wannan alkawarin ne”.[4]

 A hakikanin gaskiya yayin da mutum yake ziyartar kabarin Manzo (s.a.w) ko na Imamai kamar yana yin bai’a da alkawari da su ne cewa ba zai taba bin wata hanya ba a cikin rayuwarsa sai hanyar da suka bari.

 Ga abin da mai ziyar kabarin Manzo yake cewa: Idan Muhajirun da Ansar wadanda suka halarci yakin Hudaibiyya sun yi maka bai ‘a a kan kariya ga addini (Fathi: 18), Sannan idan matan Makka sun yi maka bai’a a kan gujewa daga yin shirka da sabon Allah (Mumtahna: 12), Idan har Muminai masu sabo sun samo umarni a kan cewa su zo wajenka domin ka nema musu gafa, ni ma ya manzon Allah ya mai ceton al’umma sakamakon halartata zuwa haraminka da sallama zuwa ga kabarinka ina mai yi maka bai’a a kan cewa zan yi kariya ga addininka sannan in yi nesa daga shirka da sabon Allah, sannan sakamakon haka ina rokonka ka neman mani gafara a wurin Allah.

 A nan dole mu fahimci cewa ziyarar kaburburan bayin Allah ya sha bamban da yawon shakatawa domin kuwa yana da manufarsa da ta sha bamban da yawon bude ido. Masu yawon bude ido suna zuwa wuri ne domin su more wa idanunsu, suna neman wurare masu kyau ko na tarihi domin su gane wa idanunsu, Saboda haka gurinsu shi ne shakatawa da hutawa, duk da cewa idan wannan bai kasance tare da sabon Allah ba, to musulunci ba ya hani da wannan. Amma masu ziyarar kaburburan bayin Allah suna yi ne domin kara samun alaka da masoyinsu da kuma jaddada alkwarinsu da shi, don haka duk wata wahala da zasu hadu da ita wajen isa zuwa gare shi koda kuwa zai kai ga su dunga gudu a cikin daji da kafafunsu ne da taka kayoyi suna iya jure wa duk hakan.

 Dan yawon bude ido yana neman abin da zai biya bukatunsa na kasantuwarsa mai rai ne shi, amma mai ziyara yana kokarin ya shayar da ruhinsa ta hanyar saduwa da masoyinsa, domin kuwa ba zai iya isa zuwa ga masoyinsa ba, sai ya mika hannunsa zuwa ga kabarinsa wanda yake dauke da kanshi da launinsa.

 Tarihi yan nuna cewa: Bayan wafatin Manzo Allah (s.a.w) wani bakauye ya shigo garin Madina sai ya zauna a gefen kabarin Manzo sai ya karanta wannan aya wadda take cewa: “Da wadanda suka zalunci kansu sun zo a gareka suka nemi gafarar Allah Sannan Manzo ya nema musu gafara da sun sami Allah mai karbar tuba mai rahma”.

 Sai wannan bakauyen balarabe ya ce: Ya kai manzon Allah gani na zo a wannan wuri domin ka nema mani gafara ina mai neman cetonka zuwa ga Allah”. A lokacin yana cikin kuka sai ya karanta wannan baiti na waka inda yake cewa:

Ya mafificin mutumin da aka bisne jikinsa a wadannan kasashe,



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 next