Ziyarar Kaburbura Masu Daraja



A nan gaba zamu yi bahasi ne a kan wadannan abubuwa guda hudu da muka ambata a sama:

Ziyarar Kabarin Muminai A Mahangar Kur’ani Da Sunna

 Ziyarar kabarin muminai musamman wadanda suke da alaka ta jini da mutum, wani abu ne wanda duk mutanen duniya sun hadu akan yin hakan domin kuwa ya dace da halitta mutum, sannan muna iya fahimtar haka daga wannan aya: “Kada ka sallaci kabarin wanda ya mutu dag cikinsu har abada, Sannan kada ka tsaya akan kabarinsa domin kuwa lallai sun kafirce wa Allah da manzonsa, Sannan sun mutu alhalin suna fasikai”. [6]

 Wannan aya mai girama tana bai wa Manzo umurnin abubuwa guda biyu kamar haka:

1-Kada ya yi salla ga wadan suka mutu daga cikinsu. “ Har abada kada ka sallaci daya daga cikinsu idan ya mutu.

2-Kada ya je a kabarinsu, domin yi musu addu’a ko makamancin haka. (kada ka tsaya akan kabarinsa).

 Bangare na biyu na wannan aya yana da muhimmanci na musamman a gare mu, wannan kuwa shi ne, shin tsayuwa a kan kabari yana nufin yayin rufewa ne ko kuwa yana da ma’ana fiye da hakan? Amma masu tafsiri suna karfafa ma’ana ta biyu ne, wanda zamu yi bayani dangane da abin da suke cewa kan hakan.

 Bidhawi yana cewa: Ma’anarsa kada ka tsaya a kan kabarinsu yayin rufewa ko ziyara. [7]

 Shi ma Suyudi a cikin tafsirul jalalaini[8] ya tafi a kan wannan ra’ayi, Sannan Arif Bursi a cikin tafsirin Ruhul Bayan[9] da Alusi Bagadadi a cikin ruhul ma’ani[10] ya kawo wannan.

 Saboda haka Allah madaukaki yana hani ga Manzo a kan ya tsaya a kan kabarin munafukai yayin rufewa ne ko kuwa domin ziyara. Wannan yana nuni ne a kan cewa Manzo ya kasance yana halartar kabarin muminai yayin rufewa ko kuwa lokacin ziyara, sannan yana yi musu addu’a. Domin kuwa idan ba haka ba, babu ma’ana a yi masa hani a kan wannan al’amari.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 next